*Typing 1 january 2019*
*Chapter 1*
*Kaduna*
Da gudu wata mota 320 kirar toyota,ta shiga cikin wani private hospital mai
suna *S&S SAFANA SPECIALIST HOSPITAL*
Cikin Hanzari matar tabude motar tafito tayi cikin asibitin da gudu tana fadin"ku
taimakamin kada y'ata ta mutu ku taimaka min.." Nurses suka biyota aguje da
gadon daukan marasa lafiya,wata matashiyar budurwa ce aka fito da ita daga
cikin motan tareda wata dattijuwan mata,tsirtsetsen cikin keta wutsul wutsul
alamar yana gab da Fitowa Ihu take zabgawa iya karfinta tareda wasu maganganu
marasa ma'ana Da Hanzari suka gungurata sai labour room,Hajiya karima takalli
Momma tace"To ai sai kira d'anki shafaffe da mai ya taho ya girbi abunda ya
shuka" tafada dawani irin izgilanci,Momma tayi murmishi irin nata kan tace"Ayyah
Hajiya zai zo ba"a gabanki namai waya ba kan mufito,insha yanxu zai zo kila wani
abun ne ya tsaidashi"Tafada tana duban Hajiyar yamutsa fuska tayi zatayi magana
kenan Kamshin turaren azzaro visit yafara musu maraba ko ba'a fada musu ba
sunsan mamallakin kamshin.
Momma takara fadada fara'arta daidai lokacin da suka kariso maza biyu ne cikin
shigar suit Black and ash,rigar likitancine saye acikin su,Daya daga cikinsu ya
Karisa yana Fadin"Momma Har kun iso?
Cikin fara"a tace"mun iso Babana kashiga sun shiga da ita ciki"mtswssss tsakin
daya katsesu kenan suka juya atare suna kallon Hajiya kari datake zabgamusu
Harara,tace cikin kallon raini"Kaga mallam ba mgana zaka tsaya yi ba yata
nakeson nasan Halin data ke cike,tundazu anshiga da ita bawani labari"Tsam
dukkansu sukayi da rai kafin momma tayi karfin halin zame Hannunta tana
Fadin"Babana Hanzarta kashiga ga Halin da *SAKINATU* take ciki.
cikin takaici da bakin ciki ya juyo wow!! abunda na Furta kenan dogon bufullatani
mai cikar zati da kamala,yanada tsawon da dan kibam murjewa,dogon Hanci ya
mallaka tareda madaidaitan dan bakinsa pick kamar yana shafa janbaki
idanunsa,bakin gashin kansa yakwanta ye luf dashi,zagayayyen sajensa
yakaramasa kwarjini Fari ne tas mai jaja din nan abun burgewa goshinsa dauke da
tabon salla wanda yake kara masa kima a idon mutane,wani siririn gilashine mai
karama Fuskarsa kyau sanye a idanunsa,kallo daya zakamai ka fahimci tsayayyan
Namiji ne mai cikar zati da Haiba
*DR SAFWAN SALE SAFANA* kenan likitan daya kware gurin kula daduk abunda
yashafi mata wato gynea Doctor wanda ke tare dashi *DR TAHIR* ne Abokine kuma Amini garesa kuma abokin aikinsa dasuke aiki akarkashin asibitin shi Dr
safwan din.
Sai da ya isa kusa da ita yadan ramkwafa yace cikin dakakkiyar murya"Barka da
zuwa Haji......."
"wai shi na tambayeka"ta katseshi "yata nake bukatar jin Halin datake ciki anshiga
da ita tundazu naji shuru'"
takareshe fada tana wani jijjiga kamar wata yar daba,yadade tsugunne kafin
yamike cikin sanyin jiki,ya Nufi kofar labour room din yasa Hannu a handle din
kenan Wata murya cikin karaji da azaba yaji tana fadin
"Allah ya isa tsakani na dakai safwan,kayi min ciki kabarni da wahala,kacemin
Haihuwa babu wuya...Gashi....Gashi kabarni da wahala kai babu abunda kasani
sai ci kamar tuwo wlh bazan sake yadda dakai ba" cikin bakin ciki da Nadama
yasaki Hannun kofar ya juya ya Fara Tafiya duk suka bishi da kallo Hajiya kari tace
cikin daga murya"Kai safwan ina zaka ko bakajin ihun da sakina takeyi ne....".Ina
ko waiwayowa baiyiba saima kara sauri dayayi har yabace daga gurin.
Cikin Takaici Hajiya kari tadaga Hannu sama tana Fadin"wayyo ni karima nashga
uku"kan ta isa kusa Da momma tana Fadin"ke wata irin uwace kinaganin
wulakancin da d'anki yayi ma y'ata ammh kin gagara mai magana,saboda yagama
cin moriyar ganga ya dirkamata ciki ko"?
Takareshe Fada Tana zaremata ido,Momma tayi mirimishi daya zaman mata jiki
kam tayi magana Dr Tahir yarigata dacewa"Am....Hajiya kiyi Hakuri i promise u
sakina Zata Haihu lafy"yana gama fadar haka ya bude Kofar Labour Room din ya
Shiga.
Dakyar Dr safwan ya karisa office dinshi cikin kunan rai,toilet yafada yasakarma
kansa shower ko kayan jikinsa bai cireba Haka ruwan keta kwararamai yafi minti
talati ahaka so yake yarage radadin dake addabansa,Haka ya Fito ruwa na diga ta
ko'ina ajikinsa kan kujrerar dake office din yafada yana maida Numfashi.
Har abada baisan yaushe zai zama mutum a idanun sakina da mahaifiyarta
ba,baisan yaushe sakina da Mahaifiyarta zasu daina cimai mutumci ba shida
mahaifiyarsa ba,baisan sai yaushene zata darajasa ta kallesa amtsayin miji ba bai
sani ba,bai sani ba,yafada da karfi idanuwansa sun canza launi.
Yafi minti Hudu acikin wannan yanayin kafin ya sake Bude idanuwansa,gabadaya
Zuciyarsa ta gama cika da wani kunci kansa na sarawa lokaci daya jijiyoyin kansa
suka Dago,kansa ya Dafe lokaci daya yana Share Ruwan Dake Diga daga saman
kansa,kafin ya sake komawa ya jingina da jikin kujeran yana maida Numfashi a
jere kamar wanda yayi gudun tsere.
Runte idanunsa yayi yana ajiyar zuciya Lokaci daya yana Saukar Da Numfashi
Daga ganin yadda yake yi zaka fahimci yanayin Dayake ciki na bacin rai da dacin
Zuciya,idanuwansa ya bude yana bin Kofar shigowa da kallo lokaci Daya
Abubuwan da suka Faru abaya suka fara dawowamai daki daki kamar alokacin
Abun ke Faruwa tamkar yana kallo cikin magijin talabijin.
*Domin samun kasancewa cikin masu karanta Sanyaya biyu na Mr Bello da Matar
Naseer kan 350 duka biyun Single 1 kuma 200 vips kuma 400 ne Duka biyu kuma
600 ne Muna maraba daku masoyanmu Sai kunzo*
Commets,share,like and vote.... *02*
*SHEKARUN BAYA* " *DR SALE HABULE SAFANA* shine cikakken sunan Mahaifin Dr Safwan wanda
d'ane ga marigayi Justice Habule safana kafin Allah yamai Rasuwa,yayi
gwagwarmaya agwannati har kawo mutuwarsa
Dr sale habule safana Haifaffan garin safana ne dake jihar katsina,yana da
shekara bakwai aduniya Allah yadauki ran mahaifinsa,Mahaifiyarsa Hajiya Maryam
wacce suke kirada Hajiya mama ita tadinga kula da danta har yagirma,Yayi
sakandiri sch dinsa a barewa college dake zaria anan kuma yahadu da Aminsa
kabir kankia ganin sun fito daga jaha daya yasanya abotarsu tafi tafiya daidai.
Bayan sun kamallah makaranta suka Fada ABU ZARIA a inda Sale ke karantan
medicine shikuma kabir political science,ammh duk da haka suna Haduwa in
basuda lectures,Haka rayuwa tacigada da tafiya Har kabir ya kammala digirin
dinsa ya dora masters dinshi shikuma alokacin sale yatafi Bautar kasa.
Sale a garin adamawa yatafi bautar kasa kuma achan Allah yahadasa da
mahaifiyar Safwan Hadiza,Hadiza mahaifaffiyar Adamawa ce bafullatanan asali,
marainiya bata uwa ba uba sai kanin mahaifinta wanda yariketa mai suna Baffa
Sani Hadiz bata zurfafa lilimi ba iyakarta sakandiri ammh masaniya littafan
Addinin muslunci tana da ilimi fiye da tunanin mai karatu bai kammala bautar
kasa ba Allah ya kulla aurensu tareda jajircewan Hajiya mama.
Lokacin da'akayi bikin kabir kankia na kasar spain yaje yin phd dinsa,sai da
yadawo yaji amininsa yayi aure hakika ya tayasa murna kwarai matuka samun
mace irin Hadiza,Macece kyakyawa dogowa mai dogon Hanci da gashi,Bayan
kammala bautar kasarsa yafara aiki da Aminu kano,Yaso ya dauki iyalansa
sukoma kano da zama Hajiya mama taki amincewa dole yasa yabarsu nan safana
yana zuwa musu weeked
Bayan kammala karatun kabir kankia yafada siyasa kadangadan akuma lokacin
iyayensa suka masa aure da yar uwarsa Karimatu,karimatu tun tana karimar
shegiyar makirace,gata bawani kyau ba bakace mummuna ga gajarta,tun tana
yarinyanta take bala'in son auren mai kudi bata shiri da takala,gata da kyashi da
hassada ga bariki kala kala dan dai babu yadda zai yine yasa yahakura ya amshi
karima.
Yafara rike mukamin sakataren gwannatin janar katsina akuma lokacin Hadiza ta
haifi Safwan Hakika tunganin Farko da karima tama Hadiza taji ta tsaneta saboda
tafita kyau uwa uba hankali Natsuwa da tarbiya kai akomai tadarata shiyasa lokaci
guda kyashi ya shigeta,batawani sakarmata sai kiga tawani yamutse yamutse
kamar taga kashi shiyasa Hajiya mama ganin Farko tace"Kabiru ina karoro
wannnan ruwan yan Duniyan"kai tsaye agabanta mirmishi kawai yayi itakuma
karima tadago tana karema Hajiya kallo ta kasan ido.
safwan yazo cikin gata,badewa mahaifinsa ya tafi london karo karatu sai da ya
shekara uku kana yadawo lokacin yazama consultand,Safwan nada shekara biyar
iyayensa suka kaisa Nigeria turkish.tunda Hadiza ta haifi safwan bata kara
Haihuwa.
Haka dai Rayuwan ta cigada juyawa cikin nasara da kwanciyar Hankali lokacin da
Safwan ya kammala secondry sch dinsa lokacin Da Allah ya karbi ran Mahafinsa
hatsari yayi ahanyarsa tadawowa daga kano hakika matuwar Dr sale Habu safasa
ta girgiza yan'uwa da abokan arzika,Alhaji kabir yaji mutuwar Amininsa matuka sai
dai Hakuri
Hajiya da Hadiza wacce Safwan kekira da Momma suka dau dangana suka maida
Hankalinsu wurin kula da safwan,Lafawar abun yasa yadage kasar malesia zuwa
karatun medicine sai da ya shafe shekara sha kana yadawo lokacin yazama
cikakken likitan mata.
Shima din da Aminun kanon ya fara aikin kan chukun chukun bude asibitinsa ya
kammala da taimakon Dady Alhaji Kabir kanki wanda yake matsayin kwashinan
ilimi ta jahar katsina. Koda bude asibitin ya kammala baida na aiki da Aminu kano ba Saida ya tattaro
Su Hajiya suka dawo garin kaduna kana ya maida Hankalinsa kan asibintinsa,Dr
tahir Aminsane wanda suka Hadu a malesia course daya suka karanta,kuma yan
kasa daya shiyasa abotarsu tayi karfo Shiyasa bayan ya kammala asibitin ya
Nemosa don Atafi tare
Alhaji kabir bai yada iyalan Dr sale ba yana kokarin ziyartarsu in yasamu dama,duk
abunda suke bukatu tunkan suyi mgana yake kawo musu Hakika shi mutumin
kirkine sai dai Karima tanajin bakincikin abunda yake musu dan dai bayya zatayi
duk da yanxu ta mallakeshi sai abunda tace yakeyi
*WACECE SAKINATU*
SAKINAT KABIR KANKIA shine cikakken sunanta yace ga kwamishina Alhaji Kabir
kankia da Hajiya karima wacce ake kira Hajiya kari,yayansu hudu salmace babba
tana aure a portharcort wani controller ne sai laila dake auren wani dan kasuwa a
kano,sai Sakina daga ita sai Ummi.
Gabadaya ya"yan Hajiya kari laila da sakina,sune suka dauko halayyanta wanda
ma harsun gyasheta Salma ce da Ummi kadai suka fita dabam,dukkansu suna da
degree sakina business admistration takaranta Tana son taga tazama yar kasuwa
tana juya kudi ahannunta shiyasa tana dawo daga london bayan ta kammala
masters dinta Mahaifinta ya tallafamata,tafara odar kaya daga dubai zuwa Nigeria
irinsu dogayen riguna da takalma da jaka,kayan maza kai duk abunda yadanganci
sawa da kwalliya,cikin lokaci Allah yasa abun albarka cikin shekara biyu sakina ta
bunkasa tayi kudi tuni takeda dankara dankara shaguna a
kano,kaduna,katsina,zamfara,da gombe,Sakina boutique and costimetics,sakinat
shoes,etc.
Gabadaya Hajiy Kari bata kula da tarbiyan yaran ba kwamishina baya zama so
komai na Hannunta,shiyasa sakina tataso tun tana karama bata kunya ga raina na
gaba da ita bata da kunya ko kadan bata iya girmama nagabada da ita ba.
Sakina bawata kyakyawa bace ta azo agani bakace gajera ammh saboda shafen
nan na yaran zamani yasa takoma Fara,Wani gajeran hanci gareta tana da dan
tudun baki,kan nan kamar Hammatar dan iska kullum cikin gashin doki
take,tanason mu'amala da abun mai kyau duk da ita din bamai kyau bace,Sakina
bata kaunar talaka ko kadan shiyasa danginsu na kanki kowa yasanta da rainin
arziki shiyasa kaf suka fita harkansu sboda Hajiya kari inrin matan nan ne masu
kyashi arziki daga ita sai mjinta da yayanta.
Sakina yar gayuce ta karshe kullum cikin shigar alfarma zaka ganta,to tazo
kaduna duba shop dinta taji zazzabi ya rufeta tana Hanya shine tafada asibitin Dr
safwan ganin farko tamai yasace zuciyarta wanda dagashi har ita basusan juna
ba saboda kowa ba kasar nan yayi karatunsa ba,Ada ta dauka wasane sai da
takoma gida kana ta tabbatar da takamu da son Dr safwan,tayi kokarin
tayakiceshi ammh hakan ya faskara,abinciken da'aka matane tagano dane gun
Aminin Abbanta.
Da tama hajiya kari magnar kin bada goyan baya acewarta baida qualities din
auren yarta,ammh sakinat taki hakura,taci gaba da shisshigemai da kissa da
kisisina,Da hajiya taga yarta taki hakura yasa tashiga tafita har soyayyah mai zafi
ta kullu atsakaninsu,Lokacin da kwamishina yaji labari yayi matukar farinciki
dasamun suriki irin Dr safwan,kuma yakara zumunci tsakaninsa da amininsa duk
da baya raye.
Da Hajiya mama taji lbr tadaga tsalle tace bata yarda ba saboda sanin mugun
halin Hajiya kari ammh Dr safwan ya tubure dole tasa ta amince ita daman
momma batada matsala cikin lokaci kankanin komai ya kammallah Amarya tatare
a gidanshi dake kaduna,mai dauke da shashi biyu daya na momma da Hajiya daya
shine mallakin sakina
Sunkwashi amarci na tsawon wata guda kafin halayyan,Sakina sufara bayyana.