AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE )


AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE )_

Murtuƙe fuska Banju ya yi ya ce

"Magaji! ba dawowa nayi ba"

"Na sani Banju! ba dawowa kayi ba,jarumar 'yata ce ta dawo da kai"

"Kaii Magaji! Kunceni! Idan ba haka ba yankin kwana ta koma toka! Dan kasan

wanene Banju! Bana da imani! Kasan karonmu da kai!" murmushi Baffa yayi yace

"Amma ni Magaji Bawa! ban gudu ba hakane Banju?" haɗe rai Banju yayi baffa ya

ci gaba da fadin

"A yanzu ko Magajiyata Aziza tsaf zan iya sakata kasheka! amma halin da ka

sakani yasa nake son kasheka da hannuna! ka fara ƙirga numfashinka daga yanzu

zuwa gobe" dariya Banju ya yi yace

"Ashe kuwa idan zaka kasheni zaka haɗa da 'yarka, karka manta gangar jiki daya

muke da ita" Baffa shima murmushi ya yi ya ce

"Duk makahon da kaji yace ayi wasan jifa yasan ya taka dutse bare mai ido kuma

kai ma kasan bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane, a wannan tafiyar kaine

makahon inaji ka manta da cewa yanzu haka Azima na da aure ko? mijinta shine

zai fiddaka daga jikinta ni kuma na kawo karshenka ta yadda ba zaka kuma

dawowa ba, kisan farko da na kasheka ban so ba, amma a yanzu ne zan kau da

ka" wani ihu Banju ya yi yana son tsincewa, Baffa yace

"Aziza!" juyowa tayi ta kalli Baffa, Baffa ya mata alama da ido, ta gya ɗa masa kai

sannan tayi gaban Banju tana shirin sake kafar da shi, da karfi ya furta mata

"BAHULAAAAA!!" a kunne yana son tada Bahula dake jikin Aziza, wani ja da baya

Aziza tayi ta dafe saitin zuciyarta da kanta, ganin haka yasa Baffa jan Aziza da

sauri ya watsa mata wani farin hoda nan Aziza ta sulale zata faɗi Nawaz bai yi

kasa a guiwa ba ya tare matarsa, da yatsa daya Baffa ya do ki goshin Banju,

kamar anyi ruwa an dauke haka Banju ya tsaya cak, Mom cikin tashin hankali ta

kama hannun Aziza wacce take kwance a jikin Nawaz ta ce

"Dan Allah Baban Aziza kayi wani abu, Aziza ta sha wuya wlh! Duk wani masifa

kanta yake afkawa dan Allah tunda ga Azima a cire mata Banju ko Aziza ta huta,

me yasa baka kashesa yanzu ba?" cikin kunya Baffa yace sabida har yanzu yana

jikin Azima, idan na kashe Banju a yanzu Azima ma ta tafi!" nan Mom ta gane

abunda Baffa ke nufi, ta kalli Hajja wacce ke tsaye a gefe tayi lullubi tana duƙe da

kai, Mom ta ce

"Nawaz shiga da Aziza cikin gida, Maman Aziza? Dan Allah ki daina ɗaurewa kina

wannan kunyar taki, ki saki jiki ki rungumi yarki, an wuce wannan zamanin kunyar,

yarki ce fa? Karki cutar da kanki kina son jin dumin yarki amma ki ta rabewa, dan

Allah bana son haka, ai gwara ki ja ta a jiki kafin na dauketa" rasssss!! gaban Hajja

ya faɗi jin mom tace zata dauke Aziza, amma bata iya furta ko da uhum bane tabi

bayan Nawaz da ya shige da Aziza, mom ta ce

"Baban Aziza zamu yi magana" Baffa ya ce

"To madalla bismillah" gefe suka koma suka kebe, mom ta ce

"A ba wa Almazeen matarsa yau suyi mu'amala ta aure dan a kawo karshen

wannan masifan, karka ce zaka biyewa kunya, wajan ceton rai babu zan can

kunya, a nema masa inda za a kai masa matarsa, a gobe ka kashe Banju,idan kuma hakan ba zai yu ba to a bamu su mu koma birni idan yaso komai ya daidaita

a can Banjun ya fita sai a kashesa a can birni sai mu tafi tare da ku, amma ya ka

ce?"girgiza kai Baffa ya yi cikin sauri ya ce

"Maganar a bar yankin nan a shiga gari akwai matsala, ba zan boye miki ba,

Almazeenu zai fuskanci kalubale wajan kusantar Azima, Banju ya wuce duk

tunaninki , kuma bayan ya kusanceta zaiyi ciwo, ba lallai bane ku a cikin gari kuna

da maganguna irin tamu ta gargajiya, ga misali a kan Aziza haka tayi ta faman

ciwo sai da ku ka zo kafin ta samu furen huriri ta warke, a nan aka fara yaƙin a nan

kuma nake so a ƙarasata,bana so a kai muku masifa kuna zaman lafiya, burin

Banju kenan ya sake barin yankin nan,ni kuwa ba zan bar haka ta faru ba ta yardan

Allah, dazu bayan munyi sallar asuba maganar da Baffa Mandi da Arɗo suka min

kenan a ba wa Almazeenu Azima yau, akwai wani gida da Arɗo yasa aka zagaye a

can kusa da wajan gari, amma akwai tsirarakun fulani a wajan kawai dai gidan ne

shi daya, yanzu haka zamu tafi da shi Almazeenu din, kafin nan zan ba shi wasu

magunguna da rubutu su sha shi da Nawazu din, dan shi ma yana da bukatar haka

tunda miji ne ga Aziza" Mom ta ce

"To ba damuwa hakan ma yayi Allah ya iya mana" Baffa ya amsa da amin, mom ta

kira Nawaz da Almazeen tace musu su bi Baffa, Malam Yunusa kuma da kanin

mahaifinsu Nawaz Alhaji Karami suna tare dasu sarki chubado da mai unguwa ori

sai hira sukeyi ana shan damemmen fura da nono, gwanin sha'awa.

@@@@@

Gidan suka je, duk da gidan kara ne amma yadda aka shirya gidan ya burge

Almazeen, tarko Baffa ya saka a ciki da waje ta yadda ko Banju ya fice a jikin

Azima ba iya guduwa zaiyi ba.

Sannan Baffa ya ba wa su Almazeen da Nawaz wasu maganguna da rubutu yace

su sha, ya basu na kariya da na sha da na wanka da na gogawa dana murzawa

dana ɗorawa duka babu wanda bai basu ba, daga nan sukayi wani gida gaba

kaɗan da na inda aka ba wa Almazeen, Baffa yace 

"Nawazu, kai ma a nan zaka zauna ka riƙe Aziza, dan a lokacin da abun da ke

jikinta zai fita zata iya shiga wani hali, zata iya fita hayyacinta, idan kuma ta

subuce zamu iya rasata na har abada dan babu abunda Banju ba zai yi ba" Nawaz

yace

"In sha Allah hakan ma ba zata faru ba Baffa, hakuri da gaskiya sune a sama,

zamuyi nasara a kan Banju bi'izinillahi ta'ala!" Baffa ya yi murmushi na jin dadin

samun sirkai kamarsu Nawaz da Almazeen, haka shi ma wannan gidan ma ya

saka matakan tsaro.

Wunin ranar kuwa Baffa bai zauna ba shiri yayi sosai ya koma asalin Garkuwa

Magaji Bawansa kyakkyawa fari dogon bafulatani mai dogon hanci da halin girma

da cikar zati da haiba.

Da daddare mom ita ce tayiwa Azima da Aziza komai,ita da Maman Beenah suka

raka Azima da Aziza, Almazeen wani irin kunya yakeji, hajja kuwa ta kasa fitowa a

bukka tana zaune tana tasbihi ga Allah, tana roƙon mai duka da ya fidda mata

yaranta lafiya, hakika ita kam ta ga jarabta.

Bayan an mikawa Almazeen Azima wacce take da ita da babu za a iya cewa duk

daya, sannan aka wuce aka kai wa Nawaz Aziza duk da shi ba wani abu bane zai

wakana a tsakaninsu.

Ko da su Mom suka koma itama ba kwanciya tayi ba, alwala tayi ta zauna ta

fuskanci gabas, Maman Beenah kuwa gadon kara ta haye tayi kwanciyarta dan

tace bacci takeji.

Baffa ma uban gayya bai ga ta zama ba balle ya rintsa dan kuwa a tsaye yake

kyam.

*AL-MAZEEEN DA BANJU AZIMA.* A bukka kuwa Almazeen zama ya yi ya kurawa Azima ido yana kallonta, shi bai ma

san ta ina zai fara ba, ya kwashi kusan mintuna talatin yana kallonta daga bisani

ya tashi ya ɗauro alwala ya yi sallah raka'a biyu, ya ciro wayarsa ya yi karatun

alkur'ani mai girma ya daga hannunsa sama yana adduoi sannan ya shafa ya miƙe

a hankali ya fara rage kayan jikinsa, wani magani da Baffa ya basa yace ya shafa a

jikinsa idan zai taba Azima, maganin ya shafa a hannunsa da dukkkan jikinsa,

yana tabata sai da ta girgiza,kwantar da ita yayi, Banju dake jikinta yana kallon

abunda ke faruwa ɗauresa kawai Baffa yayi, wani gurnani ya fara nan ya hau buge-

buge, Almazeen da iyakacin karfinsa ya fizgi kayan dake jikin Azima, nan dambe

ya kacame duk da banju yana daure amma ba shi ya hanasa kokarin yunkurin

kashe Almazeen ba shima Almazeen yaci albarkacin daure Banju da Baffa yayi

amma duk da haka yanaji a jikinsa, duk kalman da yazo bakin almazeen indai na

salati ne yin shi yake yi

,Banju bai gama sarewa ba sai da ya ga Almazeen ya yiwa Azima kaff da kayan

jikinta, yunkurin komawa maciji Banju yayi amma kafin ya fara hakan tuni

Almazeen ya karanto adduar saduwa ya fara kokarin shiga jikin Azima, wani

sarawa kansa yayi tare da wani wawan jiri dake shirin watsa shi waje daurewa yayi

ya riƙe kokaran gadon karan gam jikinsa na kyarma, nan Azima ta fara canzawa

tana zama wata halitta daban mai matukar ban tsoro da firgitarwa, kokarin zare

jikinsa yayi dan dama bai shigeta sosai ba, tunowa da maganar Baffa na cewa kar

ya kuskura ya kyale Azima har sai ta yi attisha sau uku dan duk hanyar da Banju

zai bi dan ya ga ya hana Almazeen kusantar Azima zaiyi, daga karshe kuma zai

kashesa ya kuma guduwa, tunowa da haka yasa Almazeen ya dage da iyakacin

karfinsa sakamakon b'ari da jikinsa ke yi ya shige Azima gabadaya, wani ihuu

Azima ta saka da karfi wanda sai da ya karaɗe gefe da kewayen inda suke, ta

shaƙo wuyan Almazeen wanda shi kadai yasan abunda yakeji kamar ana zare

ransa haka yakeji tsananin azaba dan harta fatarsa ji yakeyi kamar ana soya masa

shi, sake damƙar kafaɗun Almazeen Azima tayi ta dage ta saki wani attishawa

mai karfin gaske dan kuwa an karya makarin Banju tunda Almazeen ya afka

cikinta, tana yin attishawa na ɗaya tayi na biyu, na ukun ne nan wani guɗa ya hau

tashi, tana attishawar Banju wanda ya yi tsalle ya fice ta baki da hancin Azima,

ƙauuuuu! Azima taji yayinda ta wani firgita tana jan wani numfashi da iskar

duniya,da nauyin kai ta hau ware ido da kyar jin idon kamar an liƙe mata su, tana ji

tamkar yau ne uwarta ta haifeta, tana gama buɗe ido mutum ta hanga a saman

kanta, Almazeen wanda yake gaff da sumewa yana ganin ta bude ido a hankali ya

sauke bakinsa saitin kunnenta cikin mayuwacin hali da kyar ya furta

"Alhamdulillah! Wlcm back my dear wife, am so happy, u are back! i promise that i

wouldn't let any harm attack u, i will sacrifice my life to u, cox I luv u, am really luv

u, i fell in luv with u Azima! pls don't leave me alone" Almazeen na faɗi ya hau

kokarin zare jikinsa daga na Azima, a lokacin Azima taji wani mugun raɗaɗi ta

kasanta hakan ne yasa taja wani numfashin mai cike da azaba, a tare suka suma.

Banju dake tsaye yana

kallon Almazeen wanda yake son kashesa dan ya lashi takwabin sai ya kashe

Almazeen, amma inaaa ya kasa kusantar almazeen balle ya kashesa kasancewar

Almzeen mutum ne mai riƙo da ibada baya sanya.

*NAWAZ DA AZIZA.*

Sadda aka raka Aziza tsayuwa tayi a bakin bukkar taki karasowa, Nawaz na zaune

yana danna wayarsa da tun shigowarsu garin babu network ko ɗigo, ɗaga ido ya yi

ya kalleta ya ga jikinta sai rawa yakeyi, da alama tsorata tayi, a hankali ya tashi

yaje gabanta bata ma sani ba tayi zurfi a tunani, ji tayi an kama hannunta, a firgice

ta dago idonta ya haɗe da na Nawaz, ganin duk ta taburce yasa Nawaz rausaya

kai yace

"Ya haka? Jaruma a waje, matsoraciya a gabana?" ya faɗa yana matsota sosai, ja

da baya tayi tana shirin ficewa yasa hannu ya jata ta shige jiki jikinta, yasa hannunsa duka biyu ya kewayeta ta kasa kwacewa ya ce

"Ko za a watsar dani ne?" nan ma bata masa magana ba, ya ce

"Idan baki min magana ba, zan cinye bakinki" mamaki ne ya kama Aziza, oh dama

haka Nawaz yake? take tambayar kanta, bata gama yankewa ba sai da taji ya

dauketa ya ajiyeta a saman gadon kara yana shirin kwanciya a kanta tayi saurin

miƙewa zunbur tana fadin

"Sorry Hamma" murmushi ya yi a boye, ya ce

"To matso kusa dani, kin san Baffa yace na rikeki da kyau dan haka matso" ya faɗa

yana ware mata hannu alaman ta shigo cikin jikinsa, ganin yadda ya sauya fuska

ba alaman wasa yasa ta matso a hankali ta shige jikinsa ta kifa kanta a ƙirjinsa,

yasa hannu ya rungumeta da kyau yana son fassara me zuciyarsa takeji game da

Aziza.

A lokacin da Almazeen suka fara dambatuwa da Banju, a lokacin Aziza na kwance

a jikin Nawaz, lokaci daya kamar an zabureta haka ta miƙe, cikin hanzari Nawaz ya

fizgota ya maidata jikinsa ya matseta dan ya tuno da maganar Baffa da yake cewa

idan Aziza ta subuce za a iya rasata shiyasa ya kara matseta sosai a jikinsa, ihu

Aziza ta saka jin fatar jikinta na sabulewa, saurin ture Nawaz tayi ta koma gefe

tana ƙanƙame jikinta, fuskarta ne ta ji yana b'anb'arewa, hannu biyu tasa tana tare

fuskarta tare da ihu, ganin halin da take ciki yasa Nawaz saurin tashi zai zo gareta,

nan yabga masifa, daga ƙugunta abunda ya yi sama ta zama macijiya fara sol sai

kyalli take yi, sak irin wanda yake gani a mafarkinsa, hannu ta miƙa masa cikin

azaba tana fadin

"Help me plss! ka taimakeni Hamma Nawaz!" ta faɗa siffar jikinta na ƙasa na

haurawa zata zama macijiyar gabadaya, da saurin Nawaz ya rintse ido yaje ya

rungumeta ƙaƙam! Yana rungumarta ta tsaya a haka, a lokacin da Banju zai fita a

jikin Azima itama Aziza taci azaba dan nan suka hau gwada karfi da Nawaz,

hakika shima ya jikata, dan kuwa sadda abun zai fita gani ya yi wani farin abu shi

ba dutse ba shi ba tsuntsu ba ya fice ta goshin Aziza, yana fita numfashinta ya

tsaya cak yayinda ta koma mutum, haka Nawaz ya zauna riƙe da ita a jikinsa,

gab'ob'insa na masa ciwo sosai, har asuba.

Sanyin asuba ne ya fara farkar da Almazeen wanda da kyar yake iya buɗe ido

sabida nauyin da suka masa, ya jima a haka kafin da layi ya tashi ya janyo kayansa

ya saka, ya rufawa Azima jikinta, ya koma ya kwanta a gefenta yana sauke huci

mai zafi.

Baffa suna idar da sallar asuba Arɗo yace su je a duba yaran nan.

Mom aka kira dan da ita za aje Hajja ta ƙi fitowa ƙememe.

Suna zuwa gidan Hajja zata shiga da saurin Baffa ya dakatar da ita ya hanata

shiga, yace tana shiga Banju zai iya kasheta dan shi yanzu duk wanda ya samu zai

kashe ne" Baffa ne ya fara shiga cike da yarda da kansa sabida ya yi imani da

Allah ya yi riƙo da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam,duk wanda ya yi riƙo

dasu baya da fargaba a kan kowa, yana shiga kuwa Banju dake neman hanyar

guduwa a gidan tun daren jiya ya kasa sabida Baffa ya ɗaure ko ina da ina, suna

ido huɗu Baffa ya daga takwabi, Banju yace

"Magaji a gwabza idan ba tsoro! karka kasheni sai mun gwabza!" Baffa ya yi

murmushi yace idan ka so haka" 

"Zan so! amma ka ajiye takwabi" Baffa ya ce

"Ba daga yanzu zamu fara ba, kafin nan ga wannan" Baffa na faɗi ya wurgawa

Banju wani igiya nan ya daure Banju ya fito da shi, yana fitowa da shi ita kam mom

bata iya daga ido ta kalli Banju ba, dan tace mugun ji da mugun gani Allah ya

rabamu dasu, Baffa na cewa zata iya shiga da sauri ta wuce shi kuma ya wuce da 

Banju, mom na shiga ta samesu a yashe, Azima ta jijjiga sannan ta taba Almazeen

wanda jikinsa ke rawa alaman ciwo jikinsa zafi raɗauu kamar wuta, na Azima ma

akwai zafi amma na Almazeen ya fi nata, babu wani taimako da zata iya masa,

amma zata iya taimakawa Azima, dan haka ta fito ta haɗa ƙirare ta tafasa ruwan zafi, kafin ruwan ya gama sai ga jikan Ardo Sanda ya kawo wasu magunguna yace

Baffa yace idan su Hamma Almazeen da Azima zasuyi wanka a zuba musu shi a

ruwan wankan suyi wanka da shi, wannan kuma su sha, sannan a ba wa Hamma

Mazeen wannan,wannan kuma a ba wa Azima" mom ta karba tana masa

sannunsa da aika.

Mom da kanta ta taimakawa Azima tanuna mata yadda zatayi wankan tsarki,

sannan tayiwa mata wanka haka,ita dai Azima wani iri take jin kanta, riƙota mom

tayi suka shiga bukkar har yanzu Almazeen ya kasa motsi koda da yatsarsa daya

ne, taimakawa Almazeen mom tayo shima ya yi wanka ya yi sallah a zaune ya sha

magungunan da Baffa ya bada a ba shi daga nan ya hau bacci,itama Azima

maganin ta sha ta hau bacci, haka ma Aziza wanda aka aika aka ba wa Nawaz

yasha ita ma ya bata ta sha duk suka buge suka hau bacci.

Can wajan dandalin yanki Baffa yaje ya daure Banju, ko kaɗan Banju baida kyawun

halitta gani, ga girma katam da shi tamkar basamude ga baƙi fiye da misali, kai

babu ta yadda za a sunfanta zubin halittan Banju.

Bayan Baffa ya daure Banju yasa maga isar da sakon yankin kwana a kan ya

rubuta wasika yayi aike sauran yankuna ana gayyatar su izuwa kallon fafatawa a

tsakanin aljani Banju da Baffa bisa umarnin gayyatar sarkin yankin kwana wato

sarki chubaɗo, kamar irinsu yankin ja'i da yankin tudu da yankin ja'o da yankin

gangare, da yankin shani, da dai sauran yankuna.

Sadda wasika ta iskesu sun sha mamaki, kai wannan ai babban fafatawa ne a

tsakanin Magaji bawa da Maciji Banju, wanda ya yi b'arna da ta'adi a yankin

kwana, wanda ya kashe shahararrun masu kama macizai irinsu jarman macizai

dasu Innu maciji, da iro mai maganin macizai da dai sauransu, hakika duk

yankuna sun amince zasu zo ganin wannan fafatawar tsakanin mutum da

aljan,duk da wannan ba sabon abu bane a wajan Garkuwan Kwana Magaji Bawa

Arɗo.

Mom ce ta cewa Baffa dan Allah ya taimaka ya raba Aziza da Bahula ta koma

asalin cikakkiyar mutun ɗinta ta huta gaba daya, Baffa ya yi murmushi ya ce

wannan ba wata matsala ba ce, suka je gidan har zuwa yanzu suna bacci, goshin

Aziza Baffa ya riƙe ya rintse ido, attishawa Aziza tayi sannan ta fara hamma, wani

farin abu ne ya fito ta bakinta, a hankali farin abun ya koma kamar farin hayaki

haka, daga nan abun ya zama mutum wanda ake mata kallon dishi-dishi, Baffa ne

kawai yake iya ganinta dan kuwa mom ba ganinta take yi ba, kallon Baffa Bahula

tayi tana girgiza kai hawaye na zuba a idonta dan tasan Baffa kashe mata Yayanta

Banju zaiyi dan tasan ko a wasa Yayanta Banju ba zai haɗa karfinsa da kwatan

karfin da Magaji ke da shi ba,kawai dai a mugunta ne baya da lamba ta biyu, dukar

da kai Baffa yayi, daga haka Bahula ta b'ace, muryan mom Baffa yaji tana magana

"Baban Aziza? Yanzu shikenan sun warke babu wata matsala ko?"

"In sha Allahu, sun warke, amma wanda ba yanzu zaiji sauki ba wanda shi ba mu

san a ya zai farka ba shine Almazeenu, amma harta Azima zata farka lafiya

lau,kuma idan ta farka za a gaya mata gaskiyar abunda ya faru kar a boye mata

duk da abun da suka faru zata iya gani duk da ta kasance a sume amma zata iya

gani kamar mutum mai bacci yana mafarki sabida sun rayu a jiki daya da

Banju,jikin ma kuma nata ne, zata tuna komai kuma zata gane komai shiyasa za a

gaya mata sabida rashim gaya mata zai iya haifar mata da wani matsala, mom ta

gya ɗa kai tana mai tausayawa Almazeen.

Basu suka farka ba sai lokacin sallar azahar, wani ɗauuuu!! Aziza taji a kunnenta

da ta farka, zata fadi da saurin Nawaz ya riƙeta, wanda shima yanzu baya jin

komai ciwon jikin nasa ya tafi

"Kina lafiya?" Aziza ta gya ɗa kai tana gyara tsayuwarta, zuwa can ta ce

"Azima? yar uwata?" ta faɗa zata fice da sauri Nawaz ya rikota yace suyi sallah

kafin su tafi, sallan kuwa suka gabatar shi ya jasu sannan suka fita sukayi gidan da Almzeen da Azima suke, mom ma tana gidan tana kula da Almazeen wanda a

zaune ma ya ƙara gabatar da sallah, Azima kuwa tunda ta farka har tayi sallah

karo na farko a rayuwarta, bata furta ko da uffan bane kallo kawai take bin mutane

da shi abubuwa suna dawo mata kamar a mafarki haka take tariyowa, tana zaune

a kan sallayar kaba su Nawaz da Aziza suka shigo da sallama, Aziza tana ganin

Azima a kan sallaya tasa kukan farinciki tana fadin

"Azima?" daidai lokacin su Inna wuro da su Yawuro har ma da Hajja dasu Baffa

suka shigo, juyowa Azima tayi tana binsu da kallo, ganin Aziza yasa ta ce

"Aziza?" wani kuka Aziza tasa ta ƙaraso da sauri suka rungume juna ƙaƙam

"Me ya faru Aziza?" Azima ta tambaya cikin sheshsheƙar kuka

" zan gaya miki" cewar Arɗo, nan ya hau yiwa Azima bayani dalla-dalla tun fara

kisa da yaƙi da komai da barin yankin kwana har izuwa yanzu, wani kwalalo idanu

waje Azima tayi ta hau girgiza kai tana fadin

"Ni....ni....ni....ban.....ban....ban...kashe....kowa....ba.....Baffa.......bana....da niyyar

kasheka...Hajja ban miki rashin kunya ba.....Aziza...banyi faɗa dake ba.....dan Allah

kuyi hakuri..... Ban kashe kowa....ba..." duk Azima ta bi ta ruɗe mom ta jata a jiki ta

ringume tace

"Mun sani Azima,mun san cewa jinin Magaji da Jamila ba zata aikata hakan ba,

kwantar da hankalinki, ba ki kashe kowa ba,mugun nan azzalumin aljani Banju

shine ya kashe" ɗago daga jikin mom tayi tana kan ci gaba da kuka, duk da zafi da

ciwo da ƙasanta ke mata ba shi ya hanata tashi da gudu ta shige jikin hajja da

kuka ba, itama Hajja kukan takeyi, dagowa tayi ta kalli Baffa ta hau girgiza kai da

hannu tana fadin


 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form