Tame Gari 2

 



TAME GARI 2

.

wata irin bugawa kirjinsu yayi a tare inda nasir ya bude baki da niyyar

 yin ihu tace kanamin ihu bakinka zai tsaya a haka har abada gum yayi banda zufa ba abinda ke ketowa ita ko se raba ido takeyi a dole aljana habeeb dake zaune bakinsa fal da fura dan yakasa hadiyewa karasawa tayi cikin dakin yayin da dukansu yau saida sukayi fitsari dariya ce fal cikin dije amma takasa yi ta gintse kallon kwaryar gaban habeeb tayi taganta cike da fura tab wadda duk iya shansu basu isa su shanye ta ba bare ma taga 'yan binni kadan suke cin abinci ko a film in an nuno hmmm tace a zuciyarta ta furta yau zakusha azabatul ula kallon su tayi taga yadda suke makyarkyata tace wato bakwajin magana ko ? ko a cikin bil'adaman naga ku takadirai ne kun takamin yara sunacan sun sami gocewar kashi a tsakiyar kansu  amma ku kuna nan kuna shan fura ba ruwanku ko sannan danace kada ku dauki abin hawanku sai gobe shine kuka tura jibirila dan me gari ya dauko ko sbd kun raina izayar jinni toh tunda yarana suna halin jinya yanzu kuma bari in kwantar daku dan mai maganinsu ya fadamin yace sai sunyi shekara dari uku da saba'in kafin su warke abin takaicin ma gasu 'yan biyu ne ko yayesu banyi ba duk jarirai ne basu wuce shekara dari da ashirin ba gashi kunja musu jinya tun suna rarrafe dan haka tunda kuma ku biyu ne yanzu zan yi muku abinda kukayi musu kashin tsakiyar kanku zan malkwadar yadda zakuyi jinya tare 


wayyo Allah nadan girman Allah kiyi haquri wlh wlh bamu san da yaranki a gurinba dan ya rasulillahi manzon Allah sallallahu alaihi wasallam dan binta 'yar ma'aikin Allah nanfa suka shiga rokarta duk da dai shi nasiri a iya bincikensa besan da wani kashi a tsakiyar kai ba amma ba mamaki a halittar aljanu akwai shi su kuma ta tsinka musu jijiyar kai yau sun shiga uku shi wlh da yasan haka ne wlh da be zo kauyen nan ba shiyasa mamy bata son su zo a fannin habeeb ma haka kukan zuci yakeyi yayin daya saki baki furar ta zubo dan iya tashin hankali yana ciki a rayuwarsa ba abinda ya ke tsoro irin aljani yau saiga shi garin tukin ganganci irin na naseer yaje ya tsokano musu su kunji fa sharri readers🤣


katse musu tunani tayi ta hanyar ce musu zanyi muku afuwa amma da sharadi 


da sauri sukace mun amince wlh ko meye mun yadda mudai ki dena zuwa mana 


toh in kun yadda zaku shanye furar nan duka yanzu 


😳zaro ido sukayi waje tare da fashewa da kuka musamman nasir da a duniya ba abinda ya tsana irin fura 


cikin marairai ce fuska da kuka ya hada hannunsa biyu yace dan girman Allah kiyi hakuri wlh bana shsn fura danasha amai zanyi ke zan iya kwanciya ciwo ma 


oh to to tunda baka shan fura bari a sake maka hukunci zan daure cikinka kadaina kashi da fitsari tsawon shekara goma zan kanne maka ido daya zan toshe maka kofar hanci daya da rabin bakinka zan......


ya isa dan Allah kiyi hakuri wlh zan sha kafin tayi wata magana tuni sun fara shan furar inda suka dinga kokawa da ludayi a cewarta basa sha sosai zata kawo musu irin tasu ta aljanu aikuwa suka bada himma sosai inda suketa sha cikinsu ya cika dam gashi furar ko rabi batayi ba dan su a ganinsu ma kamar qarata akeyi bata ankara ba kawai taga sun fashe da kuka a tare abinda yabata dariya kenan wai babba da kuka abinda bata taba gani ba sai a talabijin dan haka batasan lokacin data kama dariya ba su suna kuka ita tana dariya gashi dai furar nan shanta suke


motsi taji alamar za'a shigo gurin ganin sun duka suna kallon fura suna kuka yasata saurin barin gurin ta labe bayan dakin dan wani lungu ta fara dirje bakin fuskarta 


da sallama malam ya shigo gurin turus yayi ganin su sai gunjin kuka sukeyi suna shan fura 


subahanallah ya fada yana me kiran sunan su jin muryar malam yasasu dagowa suna fadin yauwa malam aljana wlh tana dakin nan sun rude gaba daya yayin da itako tana jin suna aljana ta dira ta katanga tayi dakin kakarta tana fadin ni nayi gida dan nama fasa zuwa gaida bakin saida safe nazo 


au da duk kina ina ja'irar yarinya nama aza kinyi gida 


toh ban tafi ba sai yanzu nayi niyya ehee


mificin hannunta tajefo mata ta kauce tana dariya ta fice daga gidan


sosai naseer ke amai ya galabaita matuka inda hankalin malam yatashi sosai dan shima habeeb zazzabi ya rufeshi ba shiri malam yasa aka dauko mota aka nufi asibitin cikin gari dasu dan basu taimako dan shi lamarin yana bashi mamaki wai aljana kuma duka su biyu ke ganinta saida aka sa musu drip dukansu aka musu allurai kafin suka yi bacci amma a dan wannan lokacin duk sun rame 


********


tunda abin nan yafaru bata qara zuwa gidan malam megari ba dan ita tama manta da wasu baki yau kusan kwana hudu kenan tadai ga innarta na yawan zuwa gidan me gari


yau da wuri ta tashi ta share gidan tsaf duk da shekararta sha hudu yanzu amma tana aiki sosai sai dai in bata so ba yau dinma dan tanason ta bi su sadiya cikin gari dan zasuje gidan yayar sadiyar ne dan haka takevtaya inna aiki dan karta hanata


****

a gajiye suke likis sbd tafiyar kasa da suka sha dan haka tasamu gefen hanya ta zauna tana mayar da numfashi kamar wadda tayi gudu cikin tsananin gajiya ta dubi sadiya tace yaseen bazan iya qarasawa gida a kafa ba wannan ai sai in mutu kafin inkai 


to ai laifinki ne dije an bamu darinmu ta ihemu mu hau mahin kika tahi kikace a rabeta kowa ya kahe nahi to gahinan ai sawun mu ya fada mana dan ni wlh ji nakeyi kamar ba a jikina kafafuna suke ba 


toh ni uwarku ce da in nace kuyi abu he kunyi a wane dalili toh wlh duk wadda taqaramin harri banyi abu ba tace nayi hena mazgeta hegu kawai 

.gum sukayi sun san sauran dan duk wadda tace kala yanzu uwar mazga zata kaddamar musu 


kunga ku tahi mu tare me mahin ya kaimu gida 


to ina kudin ? cewar shatu 


ku zo kuji dabarar dana shirya duk suka hada ka wunansu guri daya kome suka ce oho naga dai sun rushe da dariya sannan suka mike suka fara tarar dan mashin 

sun tari mashin yakai goma ba wanda ya tsaya sai daga baya wani saurayi ya tsaya yace ina zaku ne 'yammata?


nan Gawo nawa?


toh ku bada nera sittin tunda ku uku ne 


ah ah malam cewar dije uku hamsin in yayi maka 


dariya abin yabashi wai uku hamsin dan haka yace to ku hau nan suka dane mashin dukansu sannu har suka iso cikin gawo dai dai gidan me gari inda dan wani tudu yake suka ce masa ya isa ya tsaya yanata zuba musu surutu sukuwa wannan ta kalli wannan ta kalli wannan da haka kuwa sai yaga hafsi da shatu  sun kwasa a guje dije ta yunkura yayi caraf ya riketa aikuwa dan da nan kallo yadawo garesu inda yara suka fara taruwa harda 'yan manya manya kan kace me guri ya cika dam tuni lbr ya isko gidan megari yana zaune dasu habeeb dake shirin komawa gida gobe dan Alhmdllh sun sami sauki dan megari yayita amso musu taimako maganin iska kuwa da tsari duk anyi musu shi suna zaune suna tattaunawa akan gidajen da basu je ba yau zuwa gobe zasu je na kusa kusa na nesa kuma sai sun kuma dawowa ana haka aka zo aka fadawa me gari wai ga dije can tayi sata an kamata cikin sauri ya mike duk da jikin tsufa amma kalmar tayi muni sata!!!sata fa toh meta sata ?


ganin yadda maganar ta shigeshi yasa su habeeb tambayar sa wacece dije?


kanwarku ce diyar gurin inusa


ku tashi muje duka suka miki suka bi shi 


koda suka iso gurin sun iske dandazon mutane an taru koda akaga me gari kowa ya ratse yabashi hanya ya isa gurin inda yaga dije tsaye me mashin ya rike mata hijabi itako ko a jikinta tanata gwagwiyar goruba 


rasa ma me zai ce yayi inda ya qarasa yana fadin malam dan Allah sakarta mana 


wlh baba bazan saketa ba sai an biyani kudina


nawa ne kudin naka?


naira hamsin ne


yanzu kai da duk akan nera hamsin katarawa mutane wannan jama'ar 


toh ai hakkina ne naga kuma akan sana'ata ne 


toh garin yaya kudi ya hadaku?


nan yakwashe komai yafada masa aljihu ya laluba ya ciro nera dari yabashi yace yabar canjin sannan yasaki dije malam yakama hannunta suka nufi cikin gida su habeeb sam basu lura ba dan suna waya ne da mumy sai da suka gama suka juya suka hango bayan me gari rike da hannun wata yarinya ze shiga gida nan suka nufi gidan suma 


tsaye ya tadda matansa da sauran ahlin gidan duk tsaitsaiye suna jimamin abin nan yabasu labarin ainihin abinda yafaru kowa ya kalli dije wadda har yanzu bata cewa kowa kanzil ba tanata dai cin goribarta ana haka su naseer suka shigo kasancewar dije ta juya baya nan suka tambayu meya faru nan malam ya shiga sanar dasu cikin zolaya habeeb yace tab ashe kuwa yau sai na bawa budurwar kauye kashi dai dai nan dije ta juyo akayi ko sa'a tasha kwalliyar nan sai dai yau jambaki tasaka kanta kile sabanin baya 


wani uban ihu naseer yasaki inda shima habeeb ya karba suka fara fadin gata nan itace suka kwasa da gudu sai dakin inna dudu suka rufo 


mamaki ne yakama kowa yayin da dije ta zube a gurin tanata dariya ganin haka malam ya dauka shedananta ne dan haka be bi ta kanta ba ya nufi dakin da suka rufe anyi anyi su bude sunki dije ce ta taso tazo dai dai kofar windo ta leka tace in baku bude kofar nan ba saina kwakule muku idanu da sauri suka taso suka hau kokawar bude kofa tun daga nan malam ya fahimci karatun suna budewa dije ta kara fashewa da dariya zasuyi ihu me gari ya buga musu tsawa yace dama wannan ce aljanar datake tsorata ku?


eh itace wlh itace shi kanshi me garin yaso yin dariya ganin yadda duk jikinsu ke kyarma 


to ai itace kanwarku diyar babanku inusa a shakiyancin dije nasan zata aikata fiye da haka 


dimmm sukayi gaba dayansu inda suka kai dubansu ga dije wadda ta dallaro harshe tare da yimusu gwalo tace ni ba aljanah bace gyadata kuka takemin ta zube ina shirin in tsince naji fitsari na juya inyi koda na juyo naga kun takemin ita shine nayi maganinku 


tunda tafara magana zuciyar mazan tahau lugude musamman. habeeb da yayi asarar hakorinsa guda na kasa saboda abin wayyo Allah

jikin habeeb har rawa yakeyi sbd tsananin bacin rai haka ma ga Naseer sunma rasa me zasu ce ganin yanayin da suke ciki yasa me gari rike hannunsu tare da cewa dije ta tafi gida aikuwa ko kafin ta fita saida ta qara musu gwalo kowanne a cikinsu ji yakeyi idan ya riketa zai iya shaketa har saita mutu 


malam ne ya shiga tausarsu da naseeha da nuna musu halin kuruciya ne 


dan kawai tanada kuruciya sai akace tayi wa mutane halin dabbobi cewar naseer 


kallonsa habeeb yayi kafin yace ai wannan yama wuce halin dabbobi ai sai na jakuna da tumaki irin na kauyen nan ma 


sosai ran me gari ya sosu ganin yadda kiri kiri suketa zagin dije bama hakan yafi bata mishi rai ba irin yadda yaketa tausar su amma suna ta nuna kiyayyar su gareta inda har suke fadin baxasu je gidan su ba sam kenan hakan na nufin zasu tsiro da lalacewar zumuncin gidansa hmmm lallai dole yasan abinyi dan haka baxata taba sabuwa ba tashi yayi ya barsu anan sunata mita suka fasa fitar ma ko ina


*****


kwana megari yayi yana saqa da warwara kafin daga baya ya cimma matsaya tunda asuba a masallaci da suka hadu da yaransa da jikoki gurin yun sallah ya tsayar da malam inusa yace yana son magana dashi cike da ladabi ya amsa ya tsugunna gyaran murya yayi kafin yace kasamu labarin abinda yafaru tsakanin yaran nan nawajen khamisu da dije?


eh nasamu lbr gurin su ayuba jiya da dare har na bata kashi ma sosai 


toh Alhmdllh amma banso ka daketa ba sai dai nagama yanke wani hukunci wanda ban sani ba ko zai yimaku dadi a matsayinku na iyayen khadija


insha Allahu baba duk abinda ka yanke nasan me kyau ne bazai cutar damu ba 


masha Allah Allah yayi maka albarka 


Ameen 


dama bawani hukunci na yanke ba illa na turata birni can gidan shi kamisu din inyaso tasamu ilimin zamani itama sannan su fahimci junansu da zumunci me karko dan iya jiya da suka san juna naga alamar gurbin kiyayya a idon yaran sbd kuruciya shiyasa nake son ta zauna gidansu nasan zata samu rayuwa me kyau kuma zata nutsu domin inka duba kiriniya irin ta dije abin se addu'a 


jimm yayi kafin ya nisa yace toh baba malam badamuwa Allah yasa haka yafi alkhairi sai dai mahaifiyar ita dijen sbd kasan gidansu sun tashi da akidar kin karatun boko shiyasa ko yanzu ta hana dijen tayi 


kada ka damu inka koma kace ina nemanta zanyi mata bayani da kaina insha Allah nasan zata fahimceni dan tanada saukin hali 


hakane nan yayiwa mahaifinsa sallama ya nufi gidan zuciyarsa cike da damuwa dan yana son dije kuma gashi a halin dije kauye ma ya aka kare bare binni kawai ba yadda zaiyi ne akan umarnin mahaifinsu 


ba karamin fama malam yasha ba kafin inna saudi ta fahimceshi inda daga baya ya yi mata nasiha nan ya fada mata yau zasu tafi dan harda shi 


koda aka fadawa dije abin mamaki murna ta dinga yi dan tana son rayuwar binni da kuma karatun boko dan haka ta shiga hada kayanta inda innarta ta dinga kallonta zuciyarta na tunanin inda 'yarta zata rayu gidan hajiya zahida macen dake kyamar mutane ko zuwa sukayi saita nuna a fili daga baya ma tace ta daina zuwa kuma kamar abin magani duk abinda ta ce ya zauna a gun Alhaji khamis 


'yan tafiya sun shirya tsaf yayin da ba wanda yasan da tafiyar dije har saida aka zo tfy sannan akaga da malam za'aje kowa yayi mamaki zuciyar su habeeb kamar ta buga akan dole suka yi shuru dije ta shige mota ita da malam akaita daga musu hannu inda kawayenta keta murna da kuma kewar uwar mazga yayin da dayawan mutane ke murnar ala raka taki gona 


*DIJE A BIRNI*


tunda suka shigo garin abuja ta zuro kai ta glass tana leke kamar zata fado yayin da malam keta murmushi yana tsokanarta ita kota kansa bata bi ba kallonta kawai takeyi sukuwa mazaje bakin ciki kamar ya kashe su da gayya nasir ya qara daga glass ai kuwa saida dije tayi kara dasauri malam yace lfy ?


bakomai baba malam bari zan rama 


zaki rama me?


kai dai ka bari kawai kasan bana cin bashi ba'acin nawa dole in anci nawa sai an biya 


toh Allah ya kyauta


Ameen


sun karaso gidan Alhaji khamis aljannar duniya inda cikin sa'a suka riskeshi kuwa ba karamin farin ciki yayi ba ganin dan tsohonshi a gidanshi kasancewar matar gidan ta fita shiyasa basu sameta ba nan bada bata lokaci ba me gari ya sanar da dansa komai da dalilin kawo dije kwarai ya nuna jin dadinsa inda nan take me gari ya nuna baxai kwana bazai koma dole aka sa drivrr ya mayar dashi ranar


******* me aikin gidan Alhaji ya kira ya ce tasa dije tayi wanka sannan ta bata abinci kafin hajiya ta dawo 


koda hajiya ta dawo ba karamar rigima aka kwasa ba dan saida Alhaji yayi mata jan ido kafin ta yadda da zaman dije a gidan 


yanzu aka fara zaman dije a binni yafi na kauye cakwakiya


Kude kubiyoni da comment.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form