MAGE Mai Kwanciyar Daukan Rai Littafi Na ɗaya




 _____ MAGE _____

_______________________________      

    Mai Kwanciyar Daukan Rai

  ------ Littafi --- Na ɗaya ------

              -----🔛 -----

       **★** PART (1) **★**

                   Post

         By Man Bash

.

        Zaune suke baki d'ayansu cikin fada, a kasa suke su dukansu saman tankadd'aden rerayin dake tsakiyar fadar Gabaki dayan su ba a saman tabarma suke ba


Kuma wani abu da zai baka mamaki dukansu sun tantankwashe kafafuwansu tun daga dattijon dake zaune har zuwa yar karamarsu 


Kamanninsu du iri daya ne, sun kwaso kamar mahaifinsu wanda ya haife su wanda yake zaunen cikin shigar shadda ruwan toka mai cike da kamala

Sai matarsa dake zaune gefensa fara tas matashiya domin sam bata kai shekarunsa ba bayanta da goyo tana dan jijjiga yarinyar dake dauke da wani irin gashi mai kyau a kanta wanda sun gado shi ne daga wajen mahaifinsu da yake bakin balarabe


Manyan malaman fadar ne zazzaune kusa da kujerar alfarma wacce sarki ke sama zaune ya kura musu ido daya bayan daya yana kallonsu

Dogarai ne hudu biyu gefe da gefen sarki, daya rike da wata irin bulalar dorina irin ta dukan rakumin nan murdaddiya mai taurin gaske sannan mai lauyewa wacce idan aka tsulawa mutun take zagaye jikinsa ta dannu da zafin gaske, dayan kuwa yana tsaye rike da wata jakar fata wacce ke dauke da alkur'ani mai girma ya masa kyakyawan riko


A hankali sarki ya dan daga kansa ya dan juya kan nasa hakan ya sa babban malamin da ya fi aminta da shi sannan ya fi kowa tsufa a fadar ya gyara cikin nutsuwa ya ce" Allah ya ja da rai, Allah ya jibanci lamuran sarkin garina, Allah ya huci zuciyar matashin sarkina mai cike da kamala, na miko gaisuwata ina kara jinjina da addu'ar gamawa da duniya lafiya


Sai da ya numfasa kafin ya ci gaba cike da jin nauyin maganar da zai yin duba da abin na cikin gida ne yace"

Yaran nan ne suka shigar da karan da ka bada rana yau a zo gabanka zaka wanzar da Shari'a kwana biyu da suka shige


Baki daya aka kwashi gyara kimtsi, sarki mai adalci, sarki mai zartar da hukunci a kan dukkan wanda aka cuta


Sai da ya lumshe idanuwansa cike da wani irin jan aji da wani irin cika da kamala sannan da jin kunyar dattijon dake zaune wanda ke tafe da iyalinsa baki daya sun zo a musu Shari'a kafin ya daga yan yatsunsa yana kallon babban yayan yaran da suka kawo karar mahaifinsu da kuma matarsa kan a saka musu alkur'ani a musu shinge kan aikata mugun abu a tsakani kama daga maganin asiri , zagon kasa dai da sauransu dukkan abinda zai zama na cutarwa ne


Da dan yatsansa ya yi nuni kan babban yayan nasu wanda kansa ke kasa yana cike da kunyar sarkin domin ya tabbata ya shak'a kuma a kansa zai sauke dukkan haushinsa 


Da sauri na kusa da shi ya fadi cewa" Sarki ya baka damar fadin abin da ke tafe da ku a matsayinka na ja gabansu


Sai da ya sadda kansa sannan ya dago ya sauke ajiyar zuciya, shi kansa kana ganinsa ka ga jinin sarautar domin maganar da zai yi sai da ya ringa motsa bakinsa kafin da kyar ya buda bakinsa ya ce" SUNANA  

DAYYABU BIN MUTALLAB,  mun kawo karar mahaifinmu ne wato MUTALLAB da kuma matarsa MARDIYA  domin muna so a yi mana shari'a ta adalci hakan ya saka muka nufo gidan adalci


Gaskiya ne jangori, gaskiya ne yaro jangori a nan adalci shi ke janye da ragamar komai


Ajiyar zuciya ya sauke ya ci gaba da fadin" ba wani abu ne ya kawo mu nan ba sai bukatar a yi mana tsakani da matar mahaifinmu wanda take uwa a wajenmu kan zamantakewar yau da kulun, kwarai muna fuskantar abubuwan dake gifata mana kala daban daban wa'inda suke saka mu a halin rashin nutsuwa da fadace fadace tsakaninmu da ita

Mun zo gidan nan ne dan kaine uban kowa kuma mai zartar da hukuncin da ya dace bisa tafiyar Addini,

 muna so a yi mana tsakani da ita kan maganar magani wato asiri,  kar ta shiga tsakaninmu da mahaifinmu, kar ta shiga tsakaninmu da yan uwanmu, kar ta shiga hurumin aikin mu, ko matayen mu ko kannen mu kar ta hada su da lamari na rashin samun miji, a takaice dai dukan wani shinge da ake yi a gidan nan mun zo da kokon barar mu kan a mana shi tsakaninmu da Su muma a yi musu tsakani da mu koda wani ta ji zai yi idan bata tona ba, koda wani muka saka ya mana ya ci mu!


Wasu kai suke jujjuyawa, wasun kuwa cike da mamakin yau shari'ar ta cikin gida ce amman suka yarda ake yinta a fili gaban kowa, Jangori ne da kansa sai y'ayansa duk da sun kasance fitattu kuma sanannu a duniyar rigima sai dai abin ya bada mamaki ganin ya amsa kira shi din ma da kansa

 nan da nan labari ya fara fita waje harma yan jarida suka fara garzayowa suka cika kofar gidan sarki kowa na jiran fitowarsu domin komin abinka shari'ar gidan sarki baka isa ka fitar da ita waje ba sai dai ka tsinci abinda ka tsinta a waje


Murmushi mahaifinsu ya yi a lokacin da DAYYABU ya gama magana kafin ya dago jajayen idanuwansa da suka rikide sukai ja sakamakon bacin rai ya kalli y'ayan nasa daya bayan daya sannan ya ce" Na yarda nima a min tsakani da iyalaina, Sai kuma ya rage muryarsa a hankali ya kalli sarki ya ce" Amman banda soyayarmu, ina nufin ni dai ta min a fuskana, kawai dai wanda zamu ci gaba da zama lafiya nake nufi.


Gaba daya aka shiga kallonsa, da yawa suka shiga sadda kansu cike da kunya, wasun su kuwa suka saki baki dan jin abin da ya fada, matarsa kuwa ta rausaya kanta tana sakin murmushi tana jujjuya kafafuwanta 

A lokacin ne itama ta dago kanta da wani irin sauri ta kai dubanta wajen mahaifinsu

Hannunta na hagu ta dago ta kai wajen bakinta da sauri tana mai rurruko manyan idanuwanta masu zagaye da kwallin kajal tace" lah


Sai kuma ta maida dubanta wajen sarki wanda ya sauke mata kallon da zata iya kira kallon tsana wanda kwanan duniya ita rayuwarta bata san me ta masa ta tsare masa ba ya tsaneta sannan yake kuma kan tsanarta kamar ya fidda mata rai , ba wani haduwa suke da shi ba sai jifa jifa ko idan Shari'a ta kawota ko ta rako wani amman daga irin kallon kyamar da yake jifanta da shi ta tabbata da ace mai magana ne shi ko mai zage zage da ya mata zagin da bata taba jin irinsa bama a duniyar nan 😜


Kanta ta yi gaggawar mayarwa ta sadda


Sarki ya dan yi gyaran murya yana mai duban dogari mai rike da dorina a hannunsa, sannan a zuciyarsa ya ayyana" Dama yaya za'a zo wajen fitina banda ke, must" ke dai kin saka kanki a uku, mai yiwuwa yanda fatarki keda baki haka aniyarki mh take azzaluma kawai!


Da sauri mai rike da bulalar nan ya dagata ya mata wani irin duka a jikin wajen da na yi tunanin garu ne, ashe ba garu bane an masa wani irin tsarin shafa penti ne ya hade da bangon


Karan da abun ya yi ne ya saka baki daya mutanen wajen sadda kansu kasa suna masu nutsuwa harma da hade kafafuwansu suna kara kimtsa zamansu


Sai da ya kuma dago kansa ya kara bin y'ayan da kallo kafin ya maida wajen mahaifinsu da kuma matarsa

Su goma sha uku ne, cikinsu ba wanda suke uwa daya kowanne da uwarsa sai dai wani ikon Allah kamaninsu baki dayansu ya zo daya sai dai daga fata ne wani ya fi wani haske

Kanta ya sauke dubansa, yanda take wasa da yan yatsunta kanta sadde tamkar saliha

Haka ya kuma furtawa a kasan zuciyarsa kafin ya maida dubansa wajen mai rike da alkur'anin


Hannunsa ya nuna kansa


Da sauri ya  buda alkur'annin ya ciro shi

Baki daya wajen suka kwashi kabbara hakan ya sa duk wanda ke wajen tsigar jikinsa tashi tana yam yam yam masu saurin hawaye kuwa suka  shiga sharewa


Kanta ta dago a hankali ta kai dubanta wajen alkur'anin

Kafeshi tayi da ido, har idanuwanta suka nuna mata abinda take zargi


Da sauri ta kalli yayansu, sai kuma ta maida dubanta wajen mahaifinsu wanda shima ita din yake kallo ya zabga mata harara domin cikinsu ba wanda baya jin haushi, su dukansu sun cira bata nuna ba, kuma daya bayan daya sai ya rama! 


Dan jan abin da ta gani ne ya sakata tabe bakinta ta maida dubanta wajen sarki wanda ya gama hada gabas da yamma kudu da arewa ya hade rai hakan ya tsoratar da dukkan wani wanda ke zaune a wajen itama da gaggawa ta sadda kanta tana dan bubbuga kafafuwanta kasan zuciyarta kuwa fadi take " Azalumi mai wata fuska😏


Babban malamin dake zaune ne ya gyara zamansa cikin kamala ya shiga koro bayanan saka layar wanda duk idan ya yi magana wajen sai an dauki kabbara


Irin abubuwan da aka gindaya habaici da baki ne kawai aka cire ciki kuwa harda duka aka saka hakan ya saka jikin DAYYABU yin wani irin sanyi nan da nan dana sani ta ziyarce shi yana kallon kannen nasa da ya yi imanin duk sai sun mutu ko sun kuturce a kan layar duka da aka saka musu dan wasu irin jarababun y'aya ne masu fadan bala'i, domin idan ta hadoka da su har kirari suke yiwa kansu na idan baka jinyata  mutum ba to kai ba jinin MUTALLAB bane!


Cike da tausayi ya ajiye dubansa a kanta, ya tabbata itace gawar fari domin kaf cikin kannensa babu wacce ta kaita fada , a haka kuwa kamanninta sam bata da siffar mafadaciya, sam domin kamanninta basu yi nuni da wacce zata iya yiwa wani illah ba mh


Ana gamawa wajen ya kwashi wani irin shiru, 

Sai da ya kuma jifan DAYYABU da kallon zamu hade sannan ya gyara rawaninsa hakan ya sa suka gane zai mike ne, domin dama wannan shari'ar ita ta fitar da shi, ita ta tsayar da shi, baya kananun shari'a sai idan babba ce ko wacce ta shafi ahalinsu


Kowa kansa na kasa sakamakon tashin da zai yi

A hankali ya sauko kafarsa ta dama mai dauke da takalmin fata irin na jinin sarauta amman yana da kalar fukafukin dawisu bayan ya yi addu'a a kasan zuciyarsa


Sai da ya gama sauke kafafuwansa sannan ya mike da wani irin isa da takama 

Yana mikewa da sauri sauran dogaran da suka karu suka shiga gyara masa rantsatsiyar suturar da ya saka ta yau wacce sak irin fukafukin dawisu ne, harta da rawanin da ya sha wani irin rawani ne da akaiwa adon dawisu hakan ya sa baki daya ya dauke hasken wajen 


Da sauri suka lallayu shi kuwa ya shiga takawa a hankali yana bi ta tsakiyar mutanen da suka layu


Kanta dake kasa hakama idanuwanta tana kallon kasa

A lokacin da ya kawo kafarsa daidai ita ta kasan gilashin dake fuskarsa mai hasken fari ya ga yar igiyar abin sauraron kidan da ta saka a kunnayenta tana sauraro, hakan ya sa ya dan jima a tsaye a kanta har sai da ta yi saurin dago da dubanta sai dai bata karasa kallon fusakarsa dake lullube da rawani da gilas ba ta yi saurin sadda tsumamun idanuwanta da kanta tana kallon takalminsa da ya tafi da imaninta baki daya 


Wata ajiyar zuciya mai zafi ya sauke yana ayyana tabas idan tana tunanin ta gagari kowa zai taka mata birki, a kullun ya hadu da ahalin gidansu yana mamakin irin zubin Halitar salihan mutane da akayi musu sai dai tarin jaraba dake ciciyarsu, bare ita dake dauke da irin idanuwan nan masu lumshewa da wani irin lumtu lumtu masu tudun gaske da wani irin kumbura😠


Kwafa ya yi a ransa ya ayyana ita har ta isa ta saka abin sauraron kida a lokacin da take zaune a gabansa? 


A hankali ya kuma daga kafarsa ya ci gaba da takawa har ya bar wajen wanda barin wajen kadai sai da ya dauki kusan minti talatin tashinsa zuwa tafiyarsa


Sai da ya shige sannan dogarin ya shaida masu suna iya daga kai


Kanta ta dago hade da harara ta sauke a fuskar dogarim wanda yake ta lullube kujerar sarki baima san tana yi ba


Yayansu na mikewa suma duk suka mimmike , mahaifinsu kuwa ya duka suna magana kasa kasa da malam 


Cike da bacin rai ta fara fita

Tana fita ta saka dogon takalminta fari kal mai tsinin gaske ta rike tsatsonta tana girgiza


Yayanta da sauran kannenta ne suka fito sai matar babansu a bayansu dauke da yarinyarta a goye


Da wani irin sauri ta zagaye ta koma kusa da ita ta kama goyon da sauri ta kunce hakan ya sa suka shiga kokowar kar ta kunce mata goyonta ita kuwa sai da ta kunce shi ta yi sauri ta damkawa yayarta mai dan sanyin cikin nasu wacce ke fadi" ke meye haka? Ki rufa mana asiri da laya tsakaninmu


Bata tsaya ta saurari abin da take fada ba ta juya da sauri ta karasa kusa da matar mahaifinta wacce ke tsaye da yan uwanta suma dangin bala'ine ta daga hannu ta wankawa matar mari da wani irin masifa ta shigeta da duka


Yan uwan matar babansu na ganin hakan suma suka shigeta da dukan domin ai laya tsakaninta da su aka yi ba da yan uwanta ba

Yan uwanta na ganin hakan suma suka kasa hakuri domin familynsu wata irin family ce mai wuyar fassara, a tsakaninsu suna cin kansu kamar me sai dai koda wasa basa bari a cuci dan uwansu idan kuwa aka yi gigin hakan suna iya haduwa su lallasa mutun


Wata irin kokowa ce ta kaure tsakanin dangin matar mahaifinsu da kuma su hakan ya saka babban yayan nasu dora hannayen sa a saman kansa a fili ya furta "shikenan, yau dai karshenmu ya zo, shikenan ta halakamu baki daya"


Da sauri ya karasa ya shiga janyo kannen nasa duk wanda ya yi gardama kuwa hannunsa yake dagawa ya wankawa mutun mari nan da nan sai mutun ya bar fadan, mutane kuwa suna kallon ikon Allah basu shiga ba domin kana iya shiga dan rabiya abin ya juye kanka su kuwa basa fatan fada da wannan ahali 🤷


Yana damkar hannunta itane ta karshe sai da ya kaita kusa da motarta ya saketa

Tana ta maida numfashi bata ankara ba ya daga hannunsa ya dauketa da gigitacen marin da ya sakata jin wani irin kauuu har kunnayenta suka yi kamar sun rufe tsabar saukar marin da zafi


Cike da fada ya ce" kin kashe mu! Kin kashe mu! Uban me ya kaiki marinta bayan yanzu aka mana tsakani da laya a gabanki aka dagata?


A firgice sakamakon zafin marin da ya dada mata  ta dago shanyayun idannuwanta masu matukar haske da girma ta kalle shi, kamar an mintsineta ta kwala ihu tana  fadin" karya ne! Ba cikaken bane! Bilahilazi sun daukeka wawa ba cikaken Alkur anin bane suka saka yaya DAYYABU!


Da sauri ya tsaya ya kura mata ido yanda aka yaga mata rigarta sai haki take tana hararan wajensu , sai da ya karyar da wuyansa ya sanyaya muryarsa  "A hankali ya ce" NAJEEBA?


idannuwanta ta saka cikin nasa ta ce" Na'am yaya dayyabu, na rantse maka karya yake sarkin ba na gaskiya bane suka saka, Abba ya fi karfinka kennan a kasar nan?


Hannunsa ya dago ransa bace ya dafe gaban goshinsa


Bai kuma yi mata magana ba ya juya ya ringa kama kannen nasa masu motarsu yana saka kowa cikin motarsa, baya yi maka magana sai dai ya nuna maka hanya kan ka tafi sha'anin gabanka


Sauran biyun da basu da mota ya janyo hannayensu ya kawo su ya buda bayan motar NAJEEBA ya tura su kafin ya maido hankalinsa kanta

Sai da ya kuma kallonta kafin ya ce" rigarki ta cire, kina kaisu ki tabatar kin koma gida kin saka sutura


Kai ta gyada masa tana kara cije lebenta masu mugun kyau da haske tamkar fatarta bata da wani duhu 


Juyawa ta yi ta shiga motarta

Da gangan ta ringa yin kamar motar ta ki tashi har sai da ta ga fitowar mahaifinta ta bi shi da kallo kafin ta yatsina bakinta ta turo bakin, sannan ta tada motar gannin yayansu ya karasa kusa da motar mahaifin nasu ta gyada kai ta tabata idan ya gane gaskiya ne ba zai yarda ba sai dai du abinda za'a yi a yi


Gudu take falfalawa da su a baya a zaune sanye da kayan makaranta har ta karasa babar makarantar school mai hade da islamiyya


Budewa ta yi suka fito ta buda jakarta ta basu kudin kari suka juya suka tafi cikin makarantar 


Motar ta koma ta yiwa kys ta tayar ta kama tafia

Tana tafe tana kara cije lebenta a haka har ta zo wajen danja


Sojan dake cikin motarsa wanda tun ficewarta dazu police suna tsayar da ita ta ki tsayawa shine ya fito ya zagaya wajen motar nata


Fuskarsa a hade take, sam ba annuri, yana daya daga cikin mutanen da akaiwa suna dan tsaurinsu da iko da mugun taurinsu a kan aikinsu, suna kama mai laifi koma waye, suna da haye basa yarda da raini

Sai dai kamar yanda kowani dan adam yake da point faible hakama na Mala'ila wato sunan da akai masa shine shagwababiyar mace


Da sauri ta saka hannayenta ta buda gaban motarta

Kayan kwaliya ta janyo da mugun sauri ta buda madubi ta dan duka dan kar a hangota daga gaba ta gyagyara kwalin idannuwanta, ta saka dan jan baki mai tafiya da kalar lebenta ya hadu sosai

Rigarta ta ja ta gyara ya kasance wajen da aka cira matan ya fito hakan ya sa ana gannin dan saman mamanta kadan ba da yawa ba


Zuge gilashin ta yi bayan ta yiwa fuskarta takwaf takwaf 

Da wata irin yanga ta dago dara daran idannuwanta ta sauke a kan fuskarsa, lokaci daya kamaninta na salihar mace mai fuzga ya bayanna a tare da ita

Gaban goshinta kuwa kwonce yake da wani irin ni'imtacen gashi wanda ya yi luf luf da shi


Sai da ta kara yin luuuuu da idannuwanta tamkar wacce zata sume sannan ta dauki tissu ta ringa goge idannuwanta nan da nan kuma sai kwallah ta taru

Tana kallonsa ta kara rage muryarta, dama mace ce mai karamar murya zazzak'a hakan ya sa sai da ya kara matsowa ya kashe kunne yana jin abinda take fadi" muryarta a sanyaye, sai dai yannayinta a hargitse ta ce" Allah ya huci zuciyarka sir, hatsari na yi ne cen baya hankalina tashe banma ga suna tsayar da ni ba, ka gafarceni mai laifi ce ni, idan kuwa na sauka na bada motar bani da ja domin ba wanda ya isa ya ja da iko ka


Wani fadi ya ji kansa ya kara, gilashin idanuwansa ya dan yi kasa da shi hakan ya bayannar da idannuwansa masu jan gaske ,

Murmushi yayi mata wanda ya bayanar da hakoransa masu tsawarya sannan iskar sigarin da ya zuk'a ta daki hancinta hakan yasa da sauri ta kai tissu din nan wajen hancinta ta rufe tana kokarin danne tarin dake son taso mata


Wayarsa ya miko mata yana kallonta da idannuwansa tamkar wanda yake daga maye yace" dora min numberki a nan yan mata, zan yi kiranki na fada maki yanda muka yi da su domin na fada masu su barni dake ne, kin san akwai yan iskan dake son lalata mana gari ne.


Murmushin yake ta saki tana jin cikinta na neman hautsinewa sakamakon shakar warin nan dake fitowa daga bakinsa yana dukan hancinta, a duniya idan akwai abinda ke sakata gudawa to warin baki ne, bata san wani irin rashin lafiya ne haka ba wanda idan ta shaki warin baki nan da nan cikinta ke murdawa ta nemi rikicewa harda juwa


Tana faman lumshe ido ta dora masa numbobin da bata san ko na waye bama tana masa dan murmushi ta mika masa wayar


Amsa ya yi ya kashe mata ido daya sannan ya bata hanya ta tayar da motarta ta halba bakin titi


Tana yin nisa ta sauke ajiyar zuciya a fili ta furta "Wawa kawai!" 


to fans kar dai ku manta fh yawan comments din ku shine zai tabbatar da kuna SO kafin wannan zaku rinka samun post a kaposting 2 ne a kullum ranar da babu comments sosai kuma post 1 ne,


   A kafta 😎


     Sai tomorrow kuma in sha'Allah Amma kafin wannan Nidin ne dai Man Bash nake cewa Asuba ta gari ku huta lapiya Ma'assalm

 ✍️ 

✍️

✍️

✍️

       Domin samun LITATTAFAN HAUSA Kuma Complete to ba wuya Abin da zakuyi kawai shine

Kushiga wannan shudin rubutun na kasa , sai kuyi like Na wannan page din ba sai na Rantse muku ba 

Dan duk littafin da muka fara sai mun gama shi har karshen sa matukar ana Bamu hadin kai wajen yin comments 


        (wato)👇


👉Hausa Novels Only

👉Hausa Novels Only

👉Hausa Novels Only

          👇👇👇

👉Hausa Novels Only

👉Hausa Novels Only

👉Hausa Novels Only

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form