MACE TA GARI

 


MACE TA GARI//12💎

Mace ta gari ba ta bin bokaye da 'yan tsibbu, ba ta amfani da kayan sihiri da siddabaru da surkulle, ba ta bata lokutanta a kan ababe masu karancin amfani, ba ta karya, giba, gori, shedar zur, gulma/ annamimanci da munafuncin, ba ta makirci ta cutar da wani, ba ta manta alkhairi, ba ta jiji da kai, ba ta jin ta fi wasu saboda wasu ni'imomin da Allah ya ba ta, ba ta tozarta mutane ko kaskantar da matsayinsu, ba ta munana zato ko jifan mutane da fasikanci ko munanan abu ba tare da ilimi ba, ba ta ashariya da munanan zantuka, ba ta hassada da keta, ba ta amfani da hilarta gurin cutar da abokiyar zamanta, ba mai mummunan kishi ba ce, ba ta yawan korafi da saurin kai kara da nuna gajiyawa, ba ta walakanta mutane balle ta wulakanta dangin mijinta, ta na daukan mahaifiyar mijinta a matsayin uwa a gurinta, ba ta shiga abin da bai shafeta ba, ba ta leke leke da binciken wayan miji da ma sirrikan mutane, ba ta dogewa a kan sabon Allah.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form