ƘOGON HALLAKA

 




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

           *ƘOGON HALLAKA*

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

           *Writed by meamoon*


        


*Free 


1️⃣➖2️⃣


 *Nigeria*🇳🇬

 __ƙarfe_ 1:45am  __Doctor Humaid..._ wani ƙyaƙyawan baƙin matashi ne ajin farko mai dogon hanci da manyan idanuwa da ƙaramin baki, fuskarsa kewaye yake da ƙasimba  Gudu yake sosea  cikin motar sa kirar discussion  continue addu'a yake Allah yasa kada ya makara zuwa meeting a karo na biyu, tafiyan mintuna talatin yayi, wani kungurmin jije naga ya nufa da motarsa  kan hanya doguwa local government dake jahar Kano,manya itatatuwa ne masa tsawon gaske cikin jijen,har sanda ya shigo jijen bai rage gudun da yake ba saboda hanyar batayi muni ba ga dukkan alamu motocin sun saba binta, bayan shigar sa jijen tafiyan mintuna ashirin yayi sai naga yayi parking motarsa kusa da wata a ƙogo, wani polyten leather ya dauko a ƙasar kujerar mai zaman banza jini ne ke ɗiga daga cikin leather, bayan fitar sa daga motar rufe motar yayi da key, tafiya yake cikin sauri yana haɗawa da ɗan gudu har ya isa ƙofar ƙogon sunkuyawa yayi ya sanya hannayensa bisa gwuiwuwin ƙafarsa yana mayar da numfashi, mintuna 3 ya dauka a haka daga bisani ya ɗago yana ƙarewa ƙogon kallo, kamar yau ne ya fara ganin ta,ƙogon kewaye take da wasu ƙarafuna masu matsaikacin tsawo saman kowanne ƙarfe dauke yake da gunkin kan zaki wadda wuta tana fita daga bakin gunkin, gefin hagu na ƙogon kuwa wata tukunyar ƙasa ce wacce cike take da jini, a can gefin damar ƙogon wata tukunyar ƙasar ce wadda  wani irin baƙin hayaki ke fita daga cikinta, idanuwan sa ya ɗago ya kalli saman ƙogon ƙwarangwal din kan damisa ne rataye wadda an daura masa baƙar yanki, tukunyar ƙasar da take baryar hagu ya nufa wacce take cike da jini, polyten leather dake hannunsa ya ajiye gefin tukunyar, faɗowa ƙasa yayi yiwa tukunyar sujjada sanan ya miƙe staye, sunkuyawa yayi dai-dai bakin tukunyar  hannayensa duka biyu ya sanya cikin tukunyar ya ɗibe jini,kafin yakai jinin bakinsa saida ya kirawo wasu sunayen kamar haka..... Han..ƙan..ƙan..ƙaran..ƙaƙa..ƙan..ƙan..ƙan..ƙaran.. han...ƙan....ƙan ƙaran....kiti..agadah..hakiti'a..kiti..agadahh......  


Yana gama fadin haka ya kai jinin zuwa bakin sa saida ya shanye shi tas sannan ya kuma dibar wani jini ya kai bakin sa saida ya sha sau uku sanan ya sunkuyo ya dauki leather da ya ajiye gefin tukunyar, sa'anan ya nufi dayar tukunyar wadda take fitar da baƙin hayaki zagaye  tukunyar yayi sau uku gaba ki daya kamanin sa ya sauya ya zama kamar wani dodo idanuwan sun canza kala sunyi ja wur dasu kamar gwarashin wuta fuskarsa kuwa tuni ta kumbura ta ƙara baki sai naso take, shumar kansa ta ƙara tsawo sosea girgiza kansa yayi wadda hakan yayi sanadiyar bajewar shumar tasa wadda yakai ga rufe masa fuska haƙoran sa sun ƙara tsawo bakinsa a rufe take amma hoƙorar gaba na sama da ƙasa sun fito har wajen bakin sa,haka faratar hannayen sa da ƙafafuwan sun ƙara tsawo sun zama kamar na horu, tsaye yayi a wajen tunyar na wasu mintuna kayan da yake sanye dasu sun chaza daga riga t-shirt da wando 👖 zuwa wata doguwar bakar riga takalmar dake kafafuwansa naga basu nan, hanyar shiga ƙogun ya nufa,ƙogun ta kasance baka ƙirin sosea  babu wata alamar haske a cikin ta, tafiya yake cikin duhun nan kamar wani mayunwacen zaki yana wani irin gurnani cike da ƙarfin hali nabi bayan sa tafiyan mintuna bakwai yayi surutan mutane nafara jiyu wanda na ƙasa fahimtar kalma koda daya ce, saboda ƙogon tana amsa maganar mutanin, duhun dake ƙogon ne ya fara raguwa sakamakon hasken wuta dake fita daga can cikin ƙogon, sautin muryoyin mutanin ke ƙara kusantomu,wani abu mai tsanani kaifi kamar reza na taka da ƙafata ta dama tsaye nayi ina ƙarewa wannan abun kallo wasu irin duwatsu ne a ƙasan ƙogun ƙananu jajaye masu kaifin gaske kamar reza,ɗaga idanuwa nayi na kalli cikin ƙogon mutane nagani tsaye sanye da baƙakin dogayen riguna ƙafafuwan su babu takalmi sumar kansu duk ta baje ta rufe masu fuskokinsu, sun kewaye wata babbar dutse wadda take fitar da ruwa mai tsananin duhu wato baƙin ruwa (tunda nake ban taɓa ganin baƙin ruwa ba ko jin lbr sai a littafin ƙogon hallaka)  akan dutsen kuwa wani jibgegen bakin mutum ne  mai munin gaske zaune a kan dutsen ya sunkuyar da kansa ƙasa sumar kansa ta rufe masa fuska, jikin ƙogon kuwa kewaye yake da gunkin kan zaki irin wadda take ƙofar ƙogon ita ma wanan tana fitar da wuta, wutar ce ta haska ƙogon


 Bayan shigar doctor humaid cikin ƙogon wajen mutanin nan naga ya nufa ya shiga cikin su kalaman da suke yi ne shima ya fara bin bakin su suna yi a tare, bayan wasu mintuna wanan mutumin dake zaune kan dutse naga ya ɗaga hannunsa sama yayi masu alamar su dakata shiru suka yi,umurtarsu yayi da su zauna,zama kowanne su yayi dirshat a ƙasa mikewa yayi tsaye yana ƙarewa kowanne daga cikinsu kallo,wani irin ihu yayi sanan yafara rawar ƴan bori saida ya dauki kusan mintuna goma a haka sanan ya fara magana kamar haka "yauma ma kamar kullum mun taru a wannan wajen ne saboda tabbatar da cewa kuwanne daga cikin mu ya cika alkawarin aljani  _mohju_ yanzu Ina buqatar kowanne daga cikin ku ya gabatar min da aikin sa"daga nan sun fara fitowa daya bayan daya daga mai ajiye yatsar hannun mutum sai mai ajiye kunne sai halshe kai harda zuciyar dan adam, doctor humaid kuwa wanan polyten leather da yazo da ita naga ya bude ya fiddo wani  farin yanki wadda ta zama ja zur sakamakon jinin da ya 6ata shi sai kuma mahaifa har guda bakwai wadda daga gani kasan masu waɗɗan mahaifar a yau ne aka haife su,murmushi mai ƙayatarwa naga wanan mutumin yayi sannan yace "sannu da ƙokari doctor aikin ka yana kyau, sannu ku da ƙokari kuwa ya cika alƙawarin aljani mohju haka kowennen ku zai ga sakamako mai kyau, ya ku ƴan kasuwa da kuke wanan kungiyar kasuwancin ku zata bunƙasa za ku sami riba mai yawa,ƴan siyasa kuma zakuyi nasara a takarar da kuke nima, likitoti kuma asibitin ku zata yi suna,ƴan flim da mawaka zaku zamo fitatto kuwa zai san ku za kuyi suna"haka dai yayi ta masu albishir daga bisani kuma sun gudanar da ƙayatattcen dinner wanda anci naman mutum an sha jini awanan hudu suka dauka daga bisani kuma kuwanne ya kama hanyar gidan sa,misalin karfe biyar da mintina arba'in na dare doctor yayi parking a kofar gidan sa dake G R A horn ya danna, get man din gidan wanda ya riga ya san lokacin dawowar ogan nasa Yana jin horn ya mike daga kan dardumar da yake zaune yana azkar ya fito da carbin sa a hannu yana ja har ya ƙaraso get din bai daina Jan carbin ba ya bude wa ogan sa get shi kuwa doctor ba tare da 6ata lokaci ba ya danna hancen motar sa zuwa ciki yana shiga parking lot ya nufa yayi parking din motar sa, cikin  sauri ya fito daga motar ya nufi entrance din gidan nasa sakamakon gajiyar da yayi Allah Allah yaki ya shiga ya kwanta awanne goma sha biyu ya dauka yana aiki a hospital kafin yaje wajen meeting dinsu bayan shigar sa bedroom dinsa  ko takalmin kafar sa bai cire ba yayi kwanciyar sa kan makakin bed dinsa................................


*Marocco*🇲🇦      


            _Rabat_

 _Abdelmalek Essaadi_ _University_ College of madcine...........................

Wasu kyawawan ƴan mata ne guda uku sun fito daga lecture kana ganin su kasan a gajiye suke daya daga cikin su  ta fara magana"bahijja fauwaz yace yau mu haɗo a Berlin international hotel,yaushe zaki haɗo da yasir?" cewar amina wacce aka kira bahijja tace "tomorrow evening" "okay can you please tell him kina son ku haɗo yau?" yeap" yauwa good girl" bahijja yau kece da girki pls dan Allah cook swallow for us I'm tried of  all these chips l need swallow" inji Aisha wacce tun sanda suka fara magana bata ce komai ba "kedai kam Allah ya maki sauƙi, cin abincin ke yayi yawa"cewar Amina   "ƙyale ta kawai hakuri zatayi da batun wani swallow irin wannan gajiyar da nayi take away zan mana" Aisha tace "kiyiwa Allah da Manzonsa kiyi mana abinda zai kama mana ciki"toh shikenan zanyi amma zan yi mana take away in huta da dare sai nayi mana tuwo da miya mai kyau irin ta gida Nigeria" yauwa ko kefa" cewar Aisha, parking lot ɗinda ki department dinsu suka nufa sun shiga motar su sun bar school premises din Amina ce ki driving, ta nufi restaurant bayan tayi parkin a parking lot din restaurant din bahijja ce ta fito zuwa ciki tana shiga ta nufi receptionist din da suke jire a wata kanta wanda kuwanne su shaye yaki da doguwar jallabiya sai green  airproum da suka daura kan jallabiyar, daya daga cikin su ta nufi shi tace dashi"slm kaifa ant kaifal yaum "(ykk ya yau)ana bi khair kaifa usa iduki maza turidi (Ina lfy mai kike so wani irin taimako zan maki?) uridu rahz bil dajaja  (fried rice da kaza nake so) dauyib(okay) daga nan ya parkeging mata fried rice and chicken dinta take away uku ya miko mata ita kuma ta miko masa card dinta ba tare da 6ata lokaci ba yacire kudin sannan ya miko mata card dinta,tana fita ta shiga mota bayan shigar ta Amina tayiwa motar key sun bar harabar restaurant din bata tsaya ko ina ba sai kofar gidan su horon ta danna get din gidan ta bude da kanta, batare da 6ata lokaci ba ta danna hanci motar zuwa ciki, parking lot ta nufa ta parking motar, daukar leather da bahijja tayu masu take away Aisha tayi da jakar ta, ita ta fara fita daga cikin motar bata tsaya ko ina ba sai kofar entrance din ƙyawattacen gidan nasu key ta ciro daga jakar ta ta bude kofar,gida ne tsarin ginin larabawa daga shigarka parlor ce mai matsaikacin girma, babbar window kitchen ne tana kallon kofar shiga parlor wadda babu ƙarfen bogalari bubu glass kana iya ganin komai na kitchen din, kama daga kitchen cabinet which is combination of green and orange colour, green plate orange cups which where well arrange green blender,big deep freezer, gas burner wadda sai ka shiga daga ciki zaka iya ganin sa,da dai sauran kayan amfani na kitchen,wasu ƙofufi guda biyu na azurfa na gani wadda suke kallon kofar kitchen daga gani kasan bedroom ne, kowanne bedroom dauke yake da set din bed kalar pink, a can parlor kuwa daining area nagani a gefin hagu wadda yake dauke da mini daining mai kujeru hudu, parlourn kewaye yake da kushin wadda an jera su in L shape kalar harsh and orange sai tv plasma dake manne jikin bango ga kuma set din home theater, mini center table ne a tsakiyar parlour,bangon parlour yaji harsh & milk colour penti sai shaning yake, labulayen dake parlour where also harsh.......................................


Bayan shigar Aisha ciki daining ta nufa ta ajiye leather daki hannunta, a nan parlour ta wurgar da jakarta,sanan ta nufi kitchen ta kwaso masu plate and spoon zuwa daining, haɗo wa kanta tea mai kauri gaske tayi,yana daga cikin ɗabi'arta shan tea kafin tafin taci abinci, (Aisha ƴar buzaye) ko kallon bahijja batayi ba datake mata dariya,zama tayi a daya daga cikin kujerun daining ta dauki take away daya ta juye shinkafa da kazar da ke ciki, cikin nitsuwa ta fara sipping tea dinta saida ta shanye shi tas sanan ta fara cin shikafar ta, bahijja ko wayarta  ta dauko ta kira yasir bayan sun gaisa, cikin muryarta na gogaggon mata ƴan duniya tace dashi in yana da time tana don su haɗo yau a barlin international hotel,abinka da wadda yake buƙace batare da wani dogon tunani ba ya amince mata harda cewar ya riga yayi masu booking a hork hotel kuma ba ƙaramin kudi ya kashe ba,tambayarta yayi wani time take son su haɗo tace mai zata sanar dashi in 30 minutes time sanan ta ending call din,tayi hakan ne domin tasamo damar tambayar Amina time ɗinda zata haɗo da fauwaz,ɗaki ta nufa domin tambayar Amina, bayan shigar ta ɗakin ta tarar Amina na sallah lasta wayarta tayi ta duba time ƙarfe biyu da mintuna goma cikin sauri ta nufi bathroom.......................................

Har idan littafin yana da dadi to kuyi comments da sharhi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form