KOGON HALLAKA

 




🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

                 *ƘOGON HALLAKA*

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

              *Writed by meamoon*


*Page*


9️⃣➖🔟


 _Alhamdulilah na sami_ _sauki masoyana masu yi min addu'a ina godiya sosea Allah ya bar kauna na gode_ ....... _sanan ina son sanar da fans _ɗina_ _cewar suyi min uzuri bayan sami daman yin posting kullum ba saboda wasu ƴan dalilai,zan riƙa posting sau uku a sati...ranar Litinin, Laraba,da kuma Alhamis inshallah__ 


*Ranakun posting*


*Mondays*


*Wednesdays*


*Thursdays*


Bayan shigarsa gidan mai gadi ya gani ya wanke mota ƙirar honda ''im sure she is in''ya faɗa ƙarƙashin makoshin sa, hamza mai gadi da ganinsa ya fara murmushi towel dake saƙale bisa dukin wuyan sa ya ciro ya share kumfar dake hanunsa da sauri ya ƙaraso ya cimma doctor humaid dake ƙoƙarin shiga cikin gidan ''barka da safiya yallabe an tashi lfy'' Barka dai hamza ya aiki" alhamdull mun gode Allah'' toh sannu ƙanwar tawa tana ciki ko? ranka shidadi tana nan"hannu sa yasa cikin aljihu ya ɗebe ƙudade masu yawa ya mika wa hamza da hannaye biyu ya ƙarɓa,kai tsaye doctor humaid ya nufe entrence din gidan da sallamar sa ya shigo gidan,zaune take bisa daining tana sipping tea dinta a hankali,cikin nistuwa ta ajiye cup din tea ɗinda ke hannunta sanan ta ɗago ta lalle Wada ke sallama murmushi dauke a fuskar ta amsa mai sallamar tare da fadin "sannu da zuwa yaya" yauwa ƴar ƙanwata ya fadi hakan tare da zama bisa daya daga cikin kujerun parlour daukar cup din tea nata tayi ta nufi sa,"har kin gama break din ne" ehy yaya" bayan isarta cikin parlour har ƙasa ta rusuna ta gaida shi da fara'a ya amsa mata zama tayi bisa kujera one siter dake facing ɗinsa,ƙuden da fito dashi daga mota ya miko mata yace "gashi nan tunda dai baza ki tambaye ni  ba kullum saidai na kawo maki" aiya Yaya ba haka bane ba daman akwai wata ƴar maganar da nake son muyi dakai"shiru tayi na wasu ƴan mintuna,ya ƙatse mata shurun ta hanyar faɗin "kiyi maganar ki mana ina jinki"numfasawa tayi sanan tace"yaya daman akan wannan ƙudaden ne  da kake bani duk sati,a gaskiya yaya sun yi min yawa bana iya yin wani abu mai amfani dasu duk sanda nayi ƙoƙarin yin wani abu na taimako sai na ƙasa bana ƙyauta bana sadaka, babban abinda ke damuna shine yadda ƙudaden suke ƙarewa batare da nasan abinda nayi dasu ba,yaya mai za hana ka gina makaranta koda primary ne wadda za'ayi karatun kyauta na tsawon shekaru uku ma'ana primary 1to3 sauran kuma iyayensu su biya kudin saboda taimakon ƴaƴan talakawa ''mai kike nufi'' Yaya ana nufin ka gina makaranta na primary sai ka baiwa duk dalibin da ya shiga makarantar scholarship na tsawon shekaru uku,sai iyayensu su biya masu daga primary 4to6 in kayi hakan yaya ba ƙaramin lada zaka samu ba,yaya sai kuma zancen ƴar uwata a kullum sai kace zaka binciko mana ƴanda take, a yanzu haka ina da tabbacin ta kammala jami'a ko kuma ta kusa kammalawa, ƙilama tayi aure ta tara yara duka duka tsakani na da ita shekaru biyu ne ne kawai Ni kam ban ma san yadda zatayi ka gano ta ba tun sanda take da sati daya a duniya muka rabu da ita yaya a gaskiya ina tsananin don ganin iyar uwata''ta ƙarara maganar kamar zatayi kuka, zuciyar sa kamar zata fito waje saboda zafin da take mai wai maiyasa a kullum burin fiddausi ta janyo mashi matsala ne wai wacce irin fittinane  yarinya ce, irin wanan halin nata ne yasa boka morhjo umurtarsa daya raba ta da gidan sa baki daya,a zahiri kuma yace da ita ''kwantar da hankali ki ƴar kanwata amma inso ki sani cewar a Nigeria fa muke in har na biye make na gina makarantar kamar yadda kikace toh ina mai tabbatar maki cewar hukumar E F C C zata ziyarce ni kar fa ki manta ni likita a ina na samu waddanan kuɗaɗen da har zan gina makaranta nace wai yara suyi karatu na tsawon shekaru uku kyauta a gaskiya hakan bazai yiwu ba,sai maganar ƙanwar har yanzu ina kan bincike so na san likitan da yake duty a ranar da muka yi hastari,da izinin Allah zamo gano ta ko saboda wanan sarkar inhar Allah yasa wa'inda suka tsinci ta basu cire mata Tata ba,ya fadi hakan tare da fiddo wata sarkar azurfa dake cikin rigarsa  wadda aka rubuta humaid,da sauri ya mayar da sarkar cikin rigar sa,mikewa yayi staye ya mayar da duban sa ga fiddausi yace ''ni zan wuce'' toh yaya Allah ya tsare'' bai ko amsata ba yayi wucewar sa, daukar kudin da ya bata tayita tawuce ɗaki ta ajiye kudin in a safe place san'an ta dauki bag dinta da car key sai ƴar vail ta fito zuwa compound din gidan, tana fita mai gadi tagani ya bude wa doctor humaid gete, parking lot ta nufa ta dauki motarta, bata tsaya ko ina ba sai Ahmadu Bello University Kano a department din agriculture take karatu..............................


*Maroco*🇲🇦


Ƙarfe 8:00am amina ce ta fara tashi daga barci, dalilin hasken rana da ya haska mata idanuwa,a hankali ta take bude idanunwanta har ta bude su gaba daya da sauri ta kai dubanta ga agogon dake manne jikin bangon dakin nasu ganin ƙarfe 8:00am yasa da sauri ta tashi daga bed tana mai goge idanunwanta dubanta ta kai ga bahijja da ke kwance sai barcin ta take cikin kwanciyar hankali tashin ta tayi tace"bahijja tashi mun makara gari ya wayi" kamr a mafarki bahijja taji amina na tashi ta daga barci,da dai taga kamr ba mafarki take ba saboda dukan da Amina keyi mata a firkice ta tashi ''wai menene haka Amina kike wani dukan na haka'' ba tare data amsata ba tayi wucewar ta zuwa bathroom brush tayi sanan tayi wanka sai ta dauro alwala sanan ta saya bathrope cikin mituna goma ta fito daga bathroom,tana fita bahijja ta wuceta ta shiga bathroom,mai kawai ta shafa sama sama,ta shirya cikin riga da wando na pakistan sanan ta gabatar da sallah tana idarwa kitchen ta nufa ta haɗo masu break tea ne da freid egg bayan ta gama ɗaki ta koma ta dauke daya cikin jakar kudinta ta raɓe bahijja dake sallah ta wuce Direct ɗakin da aisha ta kwana ta nufa sun kusan yin karo a kofa ''har kin tashi'' ehy kinga matsa min kitchen nake so naje  munyi late'' kwantar da hankalin ki malama na gama hada mana break in mun dawo sai kiyi lunch and dinner,yauwa ga wanan kudin ki riƙe na baki duka harda na bahijja na biya mata in mun tashi daga skol sai mu wuce kasuwa''shiru aisha tayi na wasu ƴan mintuna,sanan tace"a gaskiya amina na fara tunanin daina wannan aikin bana jin dadin yadda bahijja take treating ɗina riƙe ƙudin ki na yafe sanan magana zuwa kasuwa siya abin sadaka kowacc daga cikinku tasan hanyar kasuwa kuma kunsan irin turarukan da nake siya da sauran abubuwan in mun fita skol kuwacce taji tayi siyayyarta sanan tayi sadakarta ki samini a daining'' bin bayanta Amina tayi zuwa daining da jakar kudi a hannunta,bayan sun zauna kafin su fara cin abinci amina tace da ita ''aisha kiyi hakuri ki amsa wannan kudin ni nasan yadda zanyi da bahijja zan ce mata na daina damfarar mutane ki kadda ki ce mata komai kinsan bahijja da shigen tsoro da kuma son kudi barata iya aikin ita kaɗai ba sanan saboda tsoro da kuma don kudi,hakan zai sa tayi ta rarrashi na kan cewar mu cigaba da aikin kinga daga nan sai na sa mata sharaɗe cewar zata ringa biyan ki kafin ki tambaye ta,hakan yayi maki'' ta ƙarashi maganar tare da murmushi, cike da farin ciki aisha tace''na yarda'' yanzu dai zan ajiye make kudi a ɗaki'' a'a kada ki ajiye min a ɗaki ki ciro banɗre hudu ki samin cikin jakata sai ki kaimin sauran cikin ɗaki'' da toh Amina ta amsa mata sanan tayi  yadda tace kafin ta kai ƙudin ɗaki, bahijja ta fito daga ɗaki cikin shirin ta bayan isarta daining shiru tayi wa aisha,ganin haka yasa aisha gaida ita tace ''barka da safiya bahijja'' Barkan ki dai''cewar bahijja daga nan bubu wadda ya kuma cewa komai har sanda amina ta fito daga ɗaki sunyi break dinsu baki daya,sanan sun wuce skol kamar yadda suka saba bayan sun gama rubuta test dinsu sunyi lectures direct kasuwa suka wuce sun sayi turaruka kusan kala goma sai raguna guda uku sun sa an yanke masu tun a kasuwar an kuma gyara,daga nan sun wuce gidan marayu sun basu sadakar naman ragunan,turare kuma sun ji gidan naƙasassu sun raba wa gurago,a matukar gajeye suka dawo gida,bayan shigar su gida sunyi sallah sunci abinci da aisah ta dafa masu,kwanciya suka yi nan parlor suna huta gajiya,wayar Amina ce tayi ringing daukar wayar tayi tashi tayi daga kwanciyar da tayi tace''tab mum ta jini shiru tana kirana''amsar kiran tayi ta ƙara shi kunnen ta,''hmmm nima rabon da nayi waya da baba tun shekaran jiya'' cewar aisah daukar wayarta tayi ta dailing numbar babn ta,''kar a bar  ni a baya bara nima na kira uhmma............................


              *Vote comment*

                   _Meamoon_

Yanxu nasamu sauki zamu dunga posting Amma sai kunyi comments.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form