KOGON HALLAKA

 



🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

             *ƘOGON HALLAKA*

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

    

*Writed by meamoon*


*page*


5️⃣➖6️⃣


Cike da yanga da taku na mata ƴan duniya tasa hannunta ta ƙarbi jakar,wani irin shu'umin kallo yake mata hakan yasa ta sakar masa murmushi cikin hikima da dabara ta raɓa gifin sa ta wuce zuwa wajen da jakarta yake ta ajiye jakar kudin sannan ta juyo da saurin gaske wanda hakan ya baiwa sumarta daman watso zuwa fuskarta sauran kuma sun sauka zuwa kafaɗunta hannun damants tasa ta tattara suman  zuwa  gadon bayarta,duk abinda take kallonta kawai yake da idanuwansa wanda sun chanza kala sunyi ja sosea kamr gawarshi sakamakon sha'awar da take cin sa,da manuniyar yatsarta tayi mai nuni da yazo gareta,da saurin gaske ya nufo ta yana isowa rungumarta yayi ya wani matseta kamr za'a ƙwato ta daga garesa, bata so hakan ba amma babu yadda ta iya hanannyenta tasa ta rungume sa da kyau sannan cikin hikima ta kai hannunta na hagu wanda ta debi magani ɗazu ta goga mai maganin a tsakiyar kansa wani iri jiri ne ya fara ɗebar sa gani yayi ɗakin yana juya masa,a hankali kuma ganinsa ya kuma dishi dishi baya iya ganin wuri da kyau, fahimtar halin da ya shiga yasa ta ɗan raba sa da jikinta kallon sa take tana wata iri murmushin mugunta sanan ta shafa mai sauran maganin a ƙirjinsa,a hankali ta kwantar da shi kan centre carpet dake shimfiɗi ƙasar dakin,cikin sauri ta kalli agogon dake manne jikin bed din,"or shirt l have less than 10 minutes inba haka komai zai lalace min" dan dube dube ta fara tana ɗaga pillows din bed din manya da ƙanana dama bargon gaba daya ga dukkan alama wani abun take nima karaf idonta yake kai wayarsa dake side drower da sauri ta dauki wayar Allah ya taimake ta babu password contact dinsa ta shiga ta danna wajen search, searching sunanta tayi wato zuwairiyya sunan ƙaryar da ta bashi, delete din number tayi Allah ya taimake ta bata taɓa yarda suni yi chat dashi a social media ba sanan baida huton ta ko daya a wayar sa ajiye mai wayar tayi sannan ta nufin inda ta ajiye jakarta  daukar jakar tayi zeep din jakarta ta zuge wata babbar brown hijab naga ta dauko babu ɓata lkc ta zura, sannan ta ƙwaso duk wani abinda yake mallakinta ne tasa shi cikin jakar Allah ya taimake ta bata cire takalmanta ba jakar kudin da ya bata ta dauko,da hanunta na dama ta riƙe jakar kudin daya hannun kuma jakar da tazo dashi sanan ta sauke hijab dinta wanda ya rufe mata ko'ina har ƙafan ta ba'a iya gani da sauri ta bar ɗakin ta nufi lifter ta danna ya kai ta ƙasa sanan ta shiga..............................................


A can wajen Amina kuwa bayan shigarta ɗakin da fauwaz yake ganinsa tayi tare da wata budurwa balarabiya daga ganinta kasan ba kamila bace ba tun daga shigar da tayi,pink pant & bra ne kaɗai jikinta hakan yasa Amina fahimtar karuwa ce,zaune take bisa kan wata blue jacuzzi ta daura ƙafarta daya bisa daya,shi ko fauwaz ya wani manne a jikin ta yana wasa da sumanta, ita ko wani salon iskanci iri daban daban take mai,da sauri Amina ta dauke kanta daga kallon su da take,tun sanda ta shigo ɗakin yana sane da shigowar ta da gangan yaƙi kallon ta saboda ta ɓata masa rai ya daɗe yana jiranta haka ma nauwara duk ta ƙosa amma ya riga bata hakuri kan cewar Amina ta kusa zuwa,saboda shi mace daya bata isarsa hakan yasa ya gayyatosu su biyun,ɗan gyarar murya amina tayi dukkaninsu sunkai duban su gareta,da ɗan murmushin sa yace da ita "marhaban biki ya habibati(sanunki da zuwa abar kauna") ya faɗi hakan tare da mikewa tsaye ya nufi wajen da take tsaye ƙoƙarin rungumarta yayi tayi saurin kaucewa cike da tarin mamaki yake kallon ta kallon ta yayi na wasa ƴan sakanni sannan yayi murmushi tare da tafa hanunsa yace"oky na fahimci ki kishi kike?toh kiyi hakuri abar kaunata... amma fa kisani dukaninku ku biyun neman kuɗi kuke, sannan ina son sanar da ke cewar Ni mace daya bata gamsar dani, mata biyu  nake kusanta a lkc guda,saboda ba zaki iya tarayya dani sau ashirin a dare daya ba in kuma zaki iya toh bismilla..amma fa kafin nan akwai takardun da zaki sa hannun kar ace na kashi ki,in kin amence sai na sallame ta"wata irin shu'umin dariya tayi wadda hakan ya bashi mamaki ita budurwa tasa duk abinda yake faɗi tana jinsu saboda da larabci yake magana ita a tunanin ta amina zata tsorata kamar yadda sauran ƴan matan suke amma sai taji akasin  hakan,baki bude take kallon amina,ita ko Amina tun sanda ta shigo ɗakin take tunanin yadda zatayi da budurwa fauwaz din saboda maganin da Aisha ta haɗo masu mutum daya akeyiwa amfani dashi, wadda akyi da niyyar sa,jin furucin yasa hankali ta ya kwanta,dariyarta tayi mai isarta ta  sannan tace dashi"na amince zan iya ka dauko min takardun tare da kuɗi na saboda ina da duka ba'a taɓa jikina sai an bani kuɗi na a hannu" ta faɗi hakan tare da miko mai hanunta, har zuwa wanan lkc mamaki ne shimfiɗe a fuskar sa,daga bisani ya numfasa tare da wayancewa ɗaya kafaɗunsa alamar babu matsala sanan yace da ita"toh naji ki ƴar duniya amma kafin nan Bara na sallame waccan,ya faɗi hakan tare da nufan side drower first drower yaja ya ɗibo kuɗade dan shi kansa bai san iya adadin su ba ya mayar da drower ya rufe,juyuwa yayi ya mayar da dubar sa ga balarabiyar budurwarsa  nauwara yace da ita "ta'ali ya habibati khauzi hazal nuƙud(ma'ana tahu nan masoyiyata ki ƙarɓi wan'an kudin) bnza tayi mai saboda ta lura ƙudaden sunyi mata ƙadan  fahimtar abinda take nufi ne yasa shi murmushin gifen baki, sanan yace da ita 'zo ki ɗibi iya son ranki"kmar daman jira take hakan yasa cikin sauri ta dauki jakar ta dake

kusa da ita ta rataye shi sannan  ta nufi side drower ta ɗiba ƙudade iya don ranta doguwar rigarta ta dauko akan bed ta zura cikin sauri ta naɗe vail ɗintako sallama bata yi masuba ta sanya takalman ta bar ɗakin cike da farin cikin,ganin haka yasa shi kai duban sa ga Amina itama shi take kallo, magana yake son yi mata sai tayi saurin tarar nufashin sa tace mai" saura ni tunda ka sallame ta" yace "oky mai doka"second drower yaja ya dauki wata takarda ya maiko mata ƙarɓa tayi sanan ya ciro pen daga aljihunsa tun kafin ya maiko mata ta fisgo ta yi singing san'an tace dashi "ina ƙudade na" shiru yayi yana kallonta ganin duk ta rikice ta fata hayyaci sai zuffa da take  tuni yaji wani irin tausayin ta ya kamashi a gaskiya ta tsorata  sosea kodai baza iya bane kawai ta amsa mai saboda son ƙudi, ganin yana niman ɓata mata lokaci yasa tace dashi malm infa baka bani ƙudi na ba wallh bazan bari ka taɓa jikina ba saidai ka kira wata"murmushi yayi sanan yace da ita"kwantar da hankalin ki yanzu zan dauko maki ƙudaden ki"wrodrope ya nufa ya buɗe ya dauki jakar kudin gani yayi tana mai wani irin kallon rainin hankali yasa ya tsaya daga inda yake ya ɓude hannunwan sa alamar tambaya, fahimtar abinda yake nufi yasa ta numfasa kafin tace mai"a tunanin ka chininki bai chanza ba,20 round fa kace zaka yi,kaga kuwa tamsin kudin zakayi" murmushi ya kuma yi sanan yace "hakane"buɗan wrodrope din ya kuma yi ya dauki wata jakar iri daya da wanda ya dauko da fari ya tako har gaban ta ya miko mata amsar kudin tayi,cike da yanga da shagwaɓa da kissa tace "sukran ya Habibi" hannayensa duka biyu ya tallafo fuskar ta kissing ɗin ta yake so yayi hakan yasa tayi saurin gawar da kanta gefe,idanunwanta ne son sauko kan agogon da ke sakele jikin bed ɗin da ke ɗakin mintuna biyar kaɗai suka rage mata tayi amfani da maganin da A'isha ta haɗo masu inba haka ba asirin da ke maganin zai karye,shi ku ya ƙosa sosea hakan yasa yace da ita"lfy kk kuwa"murmushi tamai sanan tace lfy nake muje toh jin kalmar da tayi mai yasa cike da farin ciki ya nufi bed,ita ko tayi hakan ne domin ta sami damar fitar da maganin da A'isha ta haɗo masu cikin sauri ta ciro maganin da ɗibe dai-dai ƙima cikin sauri ta nufo shi gadan gadan shi ku jin alamar tafiyar mutum a bayansa yasa shi saurin waigowa daidai lokacin ta shafa mai maganin a tsakiyar kansa da kuma ƙirginsa sa,nan tabarshi tsaye ya rike kansa da hannuwansa duka biyu jiri mai ƙarfi ne ke kasar sa ko kallon sa bata yi ta daukar jakar kudin da ya bata Allah yasa takardun da tasa hannun suna tare da ita Allah ya taimake ta wayarsa tana cikin aljihun gaɓar rigar sa hakan yasa ta ciro ta Sharif numbarta da duk wani abun da ya haɗa alaƙa da ita, sanan ta bar ɗakin cikin sauri................................


Aisha ce zaune cikin motar su tana latsar laptop ita ma kana ganin ta kaga marar gaskiya CC TV din hotel take cutting duk wata alamar da zata nuna bahijja da amina sun shigo hotel din misali tayi cutting video ɗin lkcn da  sun shigo sun sami receptionist suna tambayar a hawa na nawa zazu sami ɗakin da suke nima camera dake ɗakunan samarin nasu kuwa disconnecting dinsu tayi gaba daya, fitar Amina daga cikin hotel yayi daidai da rufe laptop din Aisha,ni kuke jira ko kuyi hakuri fa kaɗan ya rage a sami matsala amma mun gode Allah komai yayi tafi daidai babu wata damuwa"cewar Amina bayan ta shiga mota "aisha ki yiwa motar nan key mu bar wajen nan kafin a sami matsala" inji bahijja dake zaune a mazaunin mai zaman banza kaman jira take hakan ya sa ta kunna motar babu ɓata lkc sun bar wajen sun kama hanyar zuwa gida..................................


         *Vote &comment*

            

               _Meamoon_

Masu yin comments Ina godiya shi yake karamin karfin guiwa

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form