*DAURIN BOYE*
*NA*
*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
HASKE WRITERS ASSO
(home of expert and perfect writers)
Tsaye yake cikin tafkekan dakin taron a gaban wani hamshaqin teburi wanda yake
dauke da aqalla ma'aikata kimanin mutuk arba'in,hannunsa guda dafe yake da
gaban teburin yayin da daya hannun yaketa wulwulgashi cike da gwanancewa duk
da baisan yana yi ba,da alama bayanin da yakewa ma'aikatan da suka bashi
dukkan nutsuwarsu ya dauki zafi,lokaci lokaci yana daga daya hannun nasa dake
dafe da teburin yana duba agogon hannunsa,wannan kadai ya isa ya nuna maka
mutum ne mai kiyaye lokaci da kuma alfanunsa.
"Is there any problem?...." Ya qarashe jimlar tasa ta qarshe yana duban fuskokin
ma'aikatan,saidai kowanne ya gamsu girgiza kai suka dinga yi daya bayan
daya,ganin haka ya sanya shi ya soma tattare kayanshi dake saman teburin tare
da bada umarnin a rufe taron da addu'a kaman yadda yake a qa'idarsa.
Shine mutum na farko da ya soma fita,shahid ya rufa masa baya suna magana
qasa qasa,a bakin hall din daya daga cikin mutanen dake tsaye a wajen ya karbi
kayan hannunsa sannan yabi bayansa har cikin elevetor wadda bata saukesu ko
ina ba sai hawan qarshe na kamfanin inda office dinsa yake.
Mahmoud ne kawai zaune cikin office din ya tasa computer a gaba da alamu wani
aiki yake ragewa mai muhimmanci Hannu mahmoud ya baiwa shahid suka gaisa
cike da alamun cikakkiyar sanayya a tsakaninsu bayan security din dake riqe da
kayan khaliphan ya aje ya fice,yayin da khalipha ya wuce kai tsaye bakin freezer ya
dauki ruwa ya sha bayan ya rage suit din jikinsa kana ya shige toilet,alwala ya
daura sannan ya dawo cikin office din ya tadda shahid da mahmoud suna
hira,wadda fiye da rabinta abinda ya shafi kasuwancinsu ne,daya daga cikin
wayayoyinshi wadda ke dauke da lambobin dukkan mutanen daya baiwa
muhimmanci a rayuwarsa lambarsu ke ciki,kai tsaye ya nufi bakin daya daga cikin
windows din dake cikin dakin office din wanda kai tsaye zaka iya kiransu da qofa
saboda kadan ne ya rage basu kai girman qofar ba,saidai glass ne zalla a jiki
wanda hakan zai baka damar gano ainihin farfajiyar companyn daga sama har
qasa.
Bugu biyu aka daga wayar,ya sauke ajiyar zuciya sallamar matar na ratsa
kunnensa,cikin sanyin murya kaman yadda halittar muryarshi take ya amsa
sallamar sannan yace"Anni...barka da warhaka"
"Barka kadai khalipha,kun fito daga taron ne?"
"Mun fito ammi,saidai aci gaba da yi mana addu'a Allah yasa mu dace"
"Ubangiji ya dafa,ya shiga lamarinku,ya zama jagora a gareku,ya albarkaci
rayuwarku". Cike da jin dadi yaketa amsawa da ameen,idanunsa lumshe yana
shafa qirjinsa yana jin zuciyaraa wasai
"Ya jikin anni?,kinsha maganinki na rana,naga lokaci yayi"murmushi ta saki cike da
qaunar yaron nata
"Khalipha kenan baka gajiya?,kaman ba awannin da suka shude muka gama waya
da kai ba,jiki alhamdulillah,magani kuma ina gama sha kiranka ya shigo"cikin
murmushi ya amsa
"Ya za'ayi na gaji da jinki anni....Allah ya qara miki lafiya mai dorewa". "Allahumma amin khalipha,Allah yayi albarka"
"Ameen anni...sai na dawo"
"Allah ya tsare" ta sake ambata cikin nuna kulawa da qauna,ya amsa sannan ya
kashe wayar yana murmushi,abubuwa da yawa na dawowa cikin kwanyarsa game
da annin tasa,zai iya cewa baiga uwa irin tashi ba,kuma baya zaton za'a
samu,anninsa da taban ce ko cikin halittun ubangiji,da wannan zancan zucin ya
qaraso inda su mahmoud suke.
Zaune yake gaban annin tashi cikin shigar qananun kaya na t shirt da
trouser,qafafunshi tanqwashe gabanshi kuma plate ne wanda ke dauke da tuwon
shinkafa miyar water leaf da ogu wadda ta wadata da ganda busashshen kifi da
kuma tsokar nama,a nutse yake cin abinci gefe guda suna hira da anni,hirar dake
nuna tsantsar shaquwa dake tsakaninsu,kallo daya zaka yi musu ka tabbatarwa
kanka lallai akwai saboda da shaquwa mai qafi tsakaninsu
"Khalipha..." Ta ambata a hankali wanda hakan yasa ya dago kanshi yana dubanta
sannan ya amsa
"Wai sau yaushe zan daina jiran ganin zuwam surukata?" Murmushi ne ya subuce
masa,sai ya aje cokalin hannunsa ya fasa kai lomar da yayi niya,cikin kulawa da
qauna yake dubanta sannan yace
"Kwanan nan anni,karki damu....addu'arki nake buqata kawai...ina son na kawo
miki surukar da zata kulamin dake,surukar da zata daukeki a matsayin
uwa....surukar da zakiji dadin zama da ita fiye dani yadda zanji" murmushi ya
subuce mata,sai ta kada kai tana dubanshi
"Allah ya baka mace ya gari wadda zata zame maka majingina.....amma banda
abin khalipha kana tunanin akwai irin wannan surukan yanzu?" Ta qarashe
managanar tana dariya qasa qasa,don har ga Allah bata dauki burinta ta cillashi
har haka ba,kullum dai addu'arta Allah ya bashi wadda zata soshi tsakani da
Allah,nagartacciyar matar aure,dan marairaicewa yayi kadan sannan yace
"Anni,kin sha gayamin ba'a fidda rai da rahamar Allah"
Kai ta jinjina cike da gamsuwa tace"wannan haka yake,ubangiji ya maka zabi ja
gari"
"Ameen" ya amsa yana daukar cokalinsa dinci gaba da cin abincinsa sannan yace
"Cikin sati na gaba haidar zai dawo gida hutu" murmushi tayi kaman ko yaushe
"Sun kammala jarabawar kenan"
"Eh sun samu hutu na wata biyu"
"Allah ya kai mana rai"
"Ameen" ya amsa yana daukar cup din daya cika da ruwa ya soma sha.
Da sauri sauri take tafiya hadi da duba agogon hannunta,qarfe tara da rabi na safe
dai dai,mintuna talatin zata qara ta makara wanda hakan dai dai yake da rasa
lacture dinta har na tsahon awa biyu.
Turus tayi gabanta na dan dokawa ganin asma'u zaune dafa'an cikin falon sanye
da kayan barci wanda hakan ke nuna ko wanka bata yi ba bare a kai ga shirin
fita,hannunta daya riqe da cup na tea tana kurba a hankali,daya hannun kuma
wayarta ce samfurin iphone 8 take latsawa,jikinta sanyaye ta qaraso gefanta ta
tsaya
"Ashe baki shirya ba anty asma'u?" Sai data shaqi iska kafin ta amsa
"Eh....sai eleven"
"Gashi goma lacturer din yake shiga..." Ta fada adamuwance,saboda daddy yana
gidan,kusan yasan lokutan fita lactures dinsu daya ne,tare suke fita su kuma dawo
tare a iya saninsa kenan,idanu ta daga ta kalleta ta watsa mata wani kallo
"Naga alamun raini na son soma shiga tsakaninmu aysha duk don saboda sharing
abun hawa da muke ko...to ki shiga taitayinki,ke kanki kinsan wutsiyar raqumi tayi
nesa da qasa,banda game game irin ja daddy da sunan zumunci saidai ki dinga
hangoni ta cikin glass,to banson zura kai in zaki wuce kije ki hau abun hawa na
haya ki wuce,dama dashi kika fi dacewa kuma dashi kika saba" tana kaiwa nan ta
maqala earpiece a kunnenta da alama kira ne ya shigo mata zata amsa.
A kasalance take takawa a harabar gidan,zuciyarta cike fal da tunani,tana
tsammanin kyautatawa na sanyawa kaso mutum koda baka sonshi,saidai ta
gefan asma'u sam ba haka bane,mommy kuwa har yau ta kasa fahimtar a wanne
aji take?,banbancin rayuwar data baro da wannan baya wuce sauyin muhalli,sutura
da ilimi data samu ba,amma baya ga haka zata iya kiran yanayin da SAMMAKAL a
wajenta
"A'ah,ina zaki a qafa aishatu?" Ta tsinkayi muryar daddy dake fitowa daga babban
falonshi da yake ganawa da baqinsa,wanda sam bata lura da shi ba saboda zurfin
tunanin da tayi,cikin hikima tayi qoqarin saisaita yanayinta,ta qaraso cike da
girmamawa
"Ina kwana daddy..." Ta soma da gaisheshi,don yau duka basu samu damar
haduwa ba,kasancewar jiya wajen goma na dare ya dawo qasar,ya kuma buqaci
mommy ta tasota saidai tanajin sa'adda da tace masa ai ayshan tayi bacci,bayan
idanunta biyu a sannan litattafanta ne a gabanta take dubawa,har lokacin data
shiga dakin asma'u ta tadata kan ta fito daddynsu ya dawo amma asma'un tayi
qememe tace ta gaji sa gaisa gobe,haka mommyn ta fito tace masa itama din tayi
bacci
"Ina zaki aysha?" Ya sake jeho mata tambayar bayan sun gama gaisawa,bata da
wata qarya da zata masa don kare asma'un wannan karon,saboda haka kai tsaye
tace
"Makaranta" agogon wayarsa ya duba sannan yace
"Ina asma'un.....ina kuma drivern naku?"kanta ta duqar qasa sannan tace
" yau akwai banbancin lokacin fitar namu ne"
Kai ya jinjina,tun da can shi ba mutum bane mai yawan sanya ido da takura
ba,hakan ya sanya abubuwa da dama kan gudana cikin gidan ayi musu
kwaskwarima a sauya musu salo a bashi a haka ya karba ba tare da ya sani ba.
Dai dai sannan usama drivansa ya turo get din gidan ya shigo,saboda ga
tsammaninsa a sannan zasu tafin,hakan ya sanya daddyn ya sallameta bayan ya
miqa mata sabbin 'yan dubu dubu guda biyar da sukayi saura a hannunsa wanda
da alama ya gama sallamar masu neman taimako ne wadan nan suka rage,tasan
baya kyauta a dawo masa da ita hakan ya sanya tasa hannu biyu ta amsa tana
jero masa godiya.
Ko cikin motar tunanin karamci irin na daddyn take,har abada kuma har ta mutu
ba zata taba manta alkhairinsa da karamcinsa gareta ba,qarar wayar usama ta
dawo da ita hayyacinta,daga jin yadda yake amsa wayar cikin daburcewa tasan
akwai magana
"Kiyi haquri ranki ya dade,yanzu zan ajeta na dawo,na dauka yau bazaki fita
bane...kiyi haquri" kalmar yayita maimaitawa,saidai hakan bai hana asma'u yi
masa tas ba harda alakoron zagi ta kuma katse wayar
"Kaga....ajjiyeni usama kaje ka daukota saina qarasa wani abun hawan" yana
bala'in ganin qimar ayshan saboda yadda take girmamashi tamkar yayanta,hakan
ya sanya yace
"Barshi kawai na qarasa dake aishatu,koda na ajekin ma na koma daukota ba tsira
zanyi ba" kai ta kada
"Ka ajenin babu komai...laifin ai zai ragu idan kace mata ajjiyeni kayi ba kamar ka
kaini ka dawo ba" haka ya gangara gefan titi bada son ransa ba ya ajeta ya juya ya
koma,ta tsaida adaidaita sahu ya qarasa da ita,idan da sabo ta jima da sabawa da
halayen asma'u,ta haddacesu tsaf,shi yasa ba komai ke bata ranta ba.
*mrs muhammad ce*