TARKON MUTUWA

 


TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Post:- AA Misau
Littafi na Shida 6
Part 6 A
.
.
Sarauniya badi'atul nauwara nata faman sharar
barci akan gado sai kawai taji hasken ranaya
dallare mata idanu
tana bude idanun ta kuwa sai tayi arba da
kawarta sarauniya anisa zaune akan kujera daf
da gadon da take kwance ta kura mata idanu
tana yi mata murmurshi
badi'atul nauwara ta mike zaune zumbur ta dubi
anisa cikin kaduwa da firgici tace
me ake ciki? ina su hatyan? ina fatan dai asirin
mu bai tonu ba
kodajin haka sai anisa ta kyalkyale da dariya
Sannan tace
ai tuni su hatyan sun shiga wata nahiyar babu
yadda za'ayi sarki shamsal ya sake ganin su
sai dai kawai zasu iya haduwa da mugayen
tarkunansa akan hanyarsu yanzu kece kadai
matsalata
cikin firgici badi'atul nauwara ta sake duban
anisa tace
tayaya akayi na zama matsala agareki?
anisa tace nan da cikar sa'a daya jal kwararrun
hadiman sarki shamsal zasu iso masa bincike
tabbas zasu iya gano wannan daki da kike ciki
yanzu
kinga kuwa idan suka ganki zargi ya tabbata
akan mu
hanya dayace zamu bi mu kawar da wannan
matsala
cikin zakuwa badi'atul nauwara ta ce wacce
hanya ce kenan?
anisa tace dolene mu batar da kamanninki yadda
babu mai shaidaki
hakan bazai taba yiwuwa ba face mun shafe gaba
dayan jikinki da bakin lalle wanda sai an kwana
bakwai ana wanke shi sannan zai fita tabbas
idan aka shafe ki dashi zata za'ayi ke bakar
fatace kuma komai kwakkwafin mutum bai isa ya
iya shaidaki ba
sai bayan sarki shamsal ya bar garinnan sannan
za'a wanke miki wannan lalle
kodajin wannan batu sai hankalin badi'atul
nauwara ya dugunzuma ainun saboda ko kadan
batason abinda zai taba lafiyar jikinta kai gani
takema kamar idan aka shafe ta da wannan lalle
shikenan har abada haka zata kasance
amatsayin bakar fata
yayin da anisa ta lura da wannan damuwa tata
saita dubeta cikin murmushi tace
indai kin yarda dani amatsayin aminiyarki to ki
cire duk wata damuwa dake ranki ko kuwa kina
tunanin cewa zan iya cutar dake ne?
kodajin wannan tambaya sai anisa tayi murmushi
cikin yake tace
haba yake kawata ai amana guda daya ce
nayarda a shafeni da wannan lalle amma ina
neman alfarma guda daya
ki sani cewa inbanda mahaifiyata duk fadin
duniyar nan babu wanda ya taba ganin tsiraicina
don haka wanda duk zaiyi wannan aiki inason ya
kasance macece kuma mai shekaru irin na
mahaifiyata...hmmmmm amma banda matan yanzu duk
samari sungama......
kodajin wannan batu sai sarauniya anisa tayi
murmushi tace
aikuwa kamar kin sani mai wannan aiki wata
kwararriyar macece wadda ahalin yanzu
shekarunta sunkai arba'in da shida duk duniya
babu wanda yakaita kwarewa a iya kunshi kuma
itace ta kirkiri wannan lalle da kanta
yanzun nan zata zo tayi miki wannan aiki ba
tareda bata lokaciba
gama fadin hakan keda wuya say sarauniya anisa
ta kama hannun sarauniya badi'atul nauwara
suka mike tsaye tare sannan ta jata suka fice
daga cikin dakin suka nufi wani bangare daban
na gidan sarautar
yar gajeriyar tafiya sukayi suka iso kofar wani
karamin daki da zuwansu sai suka tsaya chak
anisa ta dubi badi'atul nauwara ta tura kofar ta
shiga tana shiga sai zuciyarta ta buga da karfin
gaske sakamakon yin arba da ummul khairi
bakomaine ya haddasa hakanba face kasa gano
inda tasan wannan mata
tabbas ta taba ganinta a wadansu shekaru da
suka shude kuma tafi tunanin cewa tana yarinya
ne karama
nandai badi'atul nauwara ta turo kofar dakin
tasanya sakata da hannunta alokacin da ummul
khairi ta dago kai ta kura mata idanu tanayi mata
murmushi
amma idanunta cike suke da kwallah
al'amarin dayai matukar kada sarauniya badi'atul
nauwara kenan kuma ya bata mamaki
don haka batasan sa'adda ta durkusa kasa
agabantaba ta dubeta cikin girmamawa tace
yake wannan ma'abociyar kunci ina dalilin zuwan
kwallah a idanunki sakamakon ganina?
sa'adda ummulkhairi taji wannan tambaya sai
hawayenta ya zubo tace
yake 'yata yanzu ashe dama 'ya zata iya
mantawa da uwarta?
rabona dake tun sa'adda da mahaifiyarki ta kawo
ziyarar karshe nan garin
nice wacce tayiwa mahaifiyarki kunshi da kitso
harya zamana cewa munshaku ainun dake
agidana kike kwana dare da rana bama rabuwa
idan ban mantaba idan an bude gashinki akwai
wani tabon ciwon kuna da kika yi adakina da
wutar jin dumi alokacin da ake wani hunturun
sanyi
koda gama fadin hakan sai ummulkhairi ta yiwa
badi'atul nauwara nuni da wani katon madubi
dake manne ajikin bango tacè
jeki gaban wancan madubin ki kwaye keyarki mu
gani
batareda wata gardamaba sai badi'atul nauwara
taje gaban madubin ta juya masa baya ta kwaye
gashinta daya zubo kasan keyarta ai kuwa saiga
wannan tabon wutar
nantake ta tuno da inda abin ya faru
alokacin batafi shekara bakwai ba aduniya
gama tunanin keda wuya sai badi'atul nauwara
ta ruga izuwa ga ummul khairi ta rungumeta tana
mai zubar da hawaye tace
tabbas ke uwace agareni domin tun ina karama
kin wanke dukkan jikina bainda wata fargaba
atare da ke
tana gama fadin hakan ta kama cire tufafin jikinta
da kanta har sai da tayi zigidir agaban tsohuwa
ummulkhairi ita kuwa ummulkhairi saita dauko
wani akushi cike da wani bakin lalle mai kyalli
da maiko na musamman ta kama shafeshi
adukkan jikin sarauniya badi'atul nauwara
da zarar ta shafa lallen sai badi'atul nauwara
taga nan take lallen ya bushe ajikinta
kuma ya saje da fatarta tamkar dama can bakar
fatace ba faraba
al'amarin dayai dugunzuma hankalinta kenan
jikinta ya fara kyarma amma sai ummulkhairi ta
dafa kafadarta tace
kwantar da hankalinki yake 'yata kiyi sani cewa
ina wanke wannan lalle kamar yadda ruwa yake
wankè datti ajikin tufafi
dajin haka sai hankalin badi'atul nauwara ya
kwanta ta saki jikinta akaci gaba da shafeta
kafin rana ta fadi tuni hadiman sarki shamsal
kwararrun iya bincike sun hallara abirnin
askandariya
sudai wadannan hadimai su dari da ashirin da
dayane kuma an zabosune daga kasashe daban
daban acikinsu mutum dayane jal aka dauko
daga birnin bindal
gaba dayansu tsofaffin dakarun yakine wadanda
suka kware wajen iya leken asiri kuma kallo daya
zakayi musu kasan cewa yan duniya ne wadanda
sukaga jiya sukaga yau
kuma sukasan dukkan kissa da tuggun rayuwa
da isowar wadannan hadimai sai aka yi musu iso
har cikin fadar sarauniya anisa inda ta taresu
hannu biyu ta shaida musu cewa ubangidansu
sarki shamsl yanzu haka yana chan ma
$aukinsa yana barci sakamakon ya kwana yana
bincike da kansa abirnin
kodajin wannan batu sai shugaban hadiman wani
dattijo dan shekara saba'in wanda duk gashin
jikinsa farine fat babu baki sai yayi ajiyar zuciya
cikin takaici saboda yasan cewa sarkì shamsal
ya tafka kuskure na farko
nandai saraunya anisa ta dubi shugaban hadiman
tace
yanzu za'akaiku masauki domin ku je ku kwanta
ku huta kuma a kawo muku abinci
dajin haka sai shugaban hadiman yace
a'a ranki y dade ai dokar wannan aiki namu
bamacin abincin kowa sai wanda mukazo dashi ...............



TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Post:-  AA Misau
Littafi na Shida 6
Part 6 B
.
.
Muna fatan zaki bamu hadin kai bisa duk abin da
muka bukata domin idan kika ki
za'a iya samun sabani tsakanin ki da mai girma
sarki shamsal
lokacin da shugaban hadiman yazo nan
azancensa sai zuciyar anisa ta buga da karfi
domin ta fahimci cewar ta hadu da tsohon dan
duniya wanda zai iya tono asirinta amma sai ta
dake bata nuna alamar karayar taba ta dubi
Tsohon da kwarin guiwarta tace
zan baku cikakken hadin kai amma bisa irin
sharadin da ke tsakanina da sarki shamsal
sharadin kuwa shine ban yarda kuci zarafin
kowaba acikin wannan birni nawa koda kuwa
bawane mara 'yancin kansa
ku sani sarki shamsal ya amince da wannan
sharadin don haka duk wanda ya sabashi
acikinku zai fuskanci hukunci mai tsanani
kodajin wannan batu sai shugaban hadiman
tsoho lamiz ya ciza lebensa cikin alamun takaici
bai san sa'adda zancensa na zuci ya fito fili ba
yace
wannan shine kuskure na biyu da sarki shamsal
ya tafka
tsoho lamiz yayi dan tunani na tsawon yan dakiku
kadan sannan ya dubi sarauniya anisa yace
kafin mu shiga kowanne sako da lungu na
wannan gidan sarauta don gabatar da namu
binciken munaso kisa a tara gaba dayan bayi
hadimai da barorinki awancan babban fili na
wannan gida
munaso suyi layi sahu sahu na maza daban na
mata daban domin mu fara aikinmu akansu
kodajin wannan batu sai anisa tayi murmushi
tace
wannan mai sauki ne
nan take anisa ta kirawo sarkin dogarai ta bashi
wannan umarni kafin cikar sa'a daya an gama
tara wadannan hadimai acikinsu kuwa harda
sarauniya badi'atul nauwara wacce tafito
amatsayin baiwa bakar fata sanye da tufafi irin
na bayi wulakantattu
awannan lokaci badi'atul nauwara na kan gaba
alayin farko kuma acikin jerin bakaken fata ta
saje dasu babu yadda za'ayi mutum ya gane
cewa ita baiwace
lokacin da tsoho lamzis ya durfafi inda badi'atul
nauwara ke tsaye sai zuciyarta ta kama daka
domin ji take kamar lallai sai ya ganeta
tundaga nesa ya kura mata idanu ya nufota
gadan gadan harya iso daf da ita amma kuma
saiya wuceta ya dubi ta kusa da ita yayi mata
tambayoyi sannan ya kara gaba har suka gama
binciken gaba daya barori da bayi bai sake
dawowa kan badi'atul nauwara ba
adai dai wannan lokacin akaji an buga tambari
ashe sarki shamsal ne ya shigo cikin wannan
babban fili
tundazu ya farka daga barci amma sai daya gama
kintsawa sannan ya fito kai tsaye sarki shamsal
ya taho inda tsoho lamzis ke tsaye da zuwansa
sai tsoho lamzis suka russina agareshi
suka kwashi gaisuwa sannan ya dubesu cikin
fara'a yace
aikinku yayi kyau naji dadi danaga zuwanku kun
fara gabatar da aikin shin yanzu kun kammala da
wadannan hadimai ne?
dajin wannan tambaya sai tsoho lamzis ya
girgiza kai yace
a'a bamu gama da suba saura baiwa guda daya
wacce nake zargi akanta kuma nakeson nayi
mata tambayoyi
sarki shamsal ya ce wannan babu laifi kuci gba
da aikinku nizan koma masaukina idan harkun
gama gano abinda muke nema a aika min da
sauri nazo
lamzis ya rissina yace angama ya shugabana
nantake sarki shamsal ya koma masaukinsa
shikuwa tsoho lamzis saiya fito da badi'atul
nauwara da hannunsa ya kirawota ta nufo inda
yake tsaye zuciyarta tana daka
ita kuwa sarauniya anisa wacce take zaune acan
gefe daya bisa wata kujerar mulki ranta ne ya
baci
ta murtuke fuskarta kuma ta dora hannunta guda
daya akan kufen takobinta jira kawai take taga
asirinta ya tonu ta dau mataki
awannan lokaci tsohuwa ummulkhairi tana zaune
daf da ita a hannun damanta
kawai sai ummulkhairi ta dafa hannun sarauniya
anisa suka hada idanu tayi mata murmurshi gami
da kada kai alamar cewa
ta kyantar da
hamkalinta
lokacin da badi'atul nauwara ta iso daf da tsoho
lamzis saita zube kasa bisa guiwoyinta saboda
yasan cewa babu yadda za'ayi sarauniya
ta durkisa masa
tabbas tunda yaganta ya lura da tsawon ta da
kwarjininta irin na badi'atul nauwara acan
asaninsa badi'atul nauwara tana can birninta
to tayaya za'ace harta rigasu isowa nan alhalin
ita bata tsafi kuma tsafi baya tasiri akanta
abinda baisaniba shine akwai hikimar da akayi
waccan badi'atul nauwara dasuka gani ba
gaskiya bace
wata baiwace matukar kama da badi'atul
nauwara afuska datsawo amma siffofin jikinsu
sun banbanta aiun
bayan badi'atul nauwara ta durkusa agaban
tsoho lamzis a tsakaninta na bakar fata tana mai
sunkwui dakai kasa
saiya dubeta yace dago da fuskarki ki kalleni
ba tareda wata gardamaba kuwa saita dago kai
ya kura mata idanu nantake zuciyarsa ta sake
karaya domin badi'atul nauwara daya sani
kwayar idanunta fararene kal !
wannan kuwa bakine sannan waccan tana da
yalwar gashin gira
wannan kuwa dan kankanine
abinda bai sani ba shine dattijuwa ummulkhairi
ce tayi aikinta ta sanya wani abu acikin idanun
badi'atul nauwara wanda ya maida su bakake
kuma ta rage tudun gashin girarta
tsawon 'yan dakiku lamzis yana nazari da
mamaki sannan ya dubeta yaja num faa shi
ya dubeta yace tsawon shekara nawa kenan kike
bauta awannan gidan sarauta?
cikin wata irin kakkausar murya badi'atul
nauwara ta budi baki tace
tun zamanin sarki dainus mahaifin sarauniya
anisa
aka kamo mahaifiyata awajen yaki alokacin inada
shekaru hudu
kodajin wannan batu acikin wannan kakkausar
murya sai jikin tsoho Lamzis ya karayin sanyi ya
dubeta yace
tashi ki tafi banida sauran zargi akanki
hakadai su tsoho lamzis sukaci gaba da
bincikensu sai da suka shiga ko ina acikin gidan
sarautar amma basuga su hatyan ba
akarshene suka dudduba bayan gari ko zasu ga
sawun kafa kona doki mai nuna alamar cewa
basu ganiba
bayan sun kammala wannan bincikene sai tsoho
lamzis ya kadaìta dasu sarki shamsal
amasaukinsa
ya dubesu cikin nutsuwa yace ya shugabana
babu ta yadda hatyan da 'yar uwarsa zasu iya
ratsa wadannan birane har su fice daga cikin
nahiyarnan tamu ba face da taimakon wasu daga
cikin sarakunan mu
da kuma bokayenmu ayanzu nagamsu cewa
basu sami nasarar hakkaba da karfin tsafiba
lallai akwai masu mulkin dasuka munafirceka
sukayi amfani da tsananin hikimarsu da basirarsu
wajen boye wadannan makiya naka
ina ina mai tabbatar maka da cewa a yanzu su
hatyan da yar uwarsa sun shiga wata nahiyar don
haka sai kai tunani kaida bokanka kusan irin
matakin daya kamata ku dauka,
mu kam munyi iya yinmu babu sauran abinda
zamu iyayi......... yauwa sai wani jikon idan baku gajiba
munci gaba



TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Post:- AA Misau
Littafi na Shida 6
Part 6 C
.
.
Koda tsoho lamzis yazo nan azancensa sai
zuciyar sarki shamsal ta kama tafarfasa kamar
zata kone saboda tsananin fushi don haka sai ya
takarkare ya kwarara uban ihu dakyar boka arzur
da tsoho lamzis suka rarrasheshi ya dawo cikin
hayyacinsa sannan tsoho lamzis ya dubi boka
arzur yace
yanzu saikayi bincike ka gano inda su hatyan
suke ayanzu kusan abinda zakuyi
kodajin haka sai zuciyar boka arzur ta buga da
karfi tsoro ya da baibayeshi saboda yasan cewa
tsafinsa yaki yayi tasiri awannan birni kuma bai
gayawa sarki shamsal gaskiyar al'amarin ba
adai dai wannan lokaci dasu sarki shamsal
sukeyin wannan tattaunawa ne sarauniya anisa
ta dauki sarauniya badi'atul nauwara tareda
dattijuwa ummulkhairi ta fitar dasu daga cikin birnin
gaba daya ta wata barauniyar hanyar daban
wacce tasa aka basu dawakai da guziri suka
nausa daji suna masu tunkarar birnin sarauniya
badi'atul nauwara kafin suyi bankwana saida
badi'atul nauwara ta dubi sarauniya anisa cikin
alamun tsananin damuwa gami da karayar zuciya
tace yake kawata hakika bansan irin godiyar
dazan miki ba bisa hadin kan da kika bani wajen
kubutar da wadannan marayu wato hatyan da yar
uwarsa sadirat babu abinda zance sai fatan
alheri agareki idan baki mantaba abaya kince
dani nayi tunani akan yadda zamu dinga bawa su
hatyan kariya bayan sunbar wannan nahiyar har
izuwa lokacinda hatyan zai iya dawowa ya dauki
fansa akan sarki shamsal
nikam banyi tunanin komaiba akan hakan amma
nasan cewa ke tuni kinyi kuma kinyi shiru akan
hakan saboda haka nabar miki amanar hatyan
kodajin haka sai mamaki ya turnuke anisa tayi
shiru kamar bazata ce komaiba daga chan kuma
sai ta dubeta tace bazan iya karbar wannan
amanarba face kin amsa tambayar danayi miki
abaya
cikin matukar kaduwa badi'atul nauwara tace
wace tambaya kenan?
anisa tace shin kin kamuda son jarumi hatyan
ne?
badi'atul nauwara tayi ajiyar numfashi tace
saboda me kikayi mini wannan zargin kuma me
yasa kike son sani?
anisa ta sake yin murmushi tace
saboda me zaki amsa mini tambaya ta da
tambaya?
badi'atul nauwara ta kada kai tace mubar
wannan maganar yanzu kawata kije ki aiwatar da
duk abinda kike ganin cewa ya kamata
tana gama fadin hakan saita kada linzamin
dokinta ta juya ta nausa cikin daji cikin hanzari
ummulkhairi ta kada na ta dokin da sauri ta bita
abaya
ita kuwa sarauniya anisa hankalintane ya
dugunzuma tabi badi'atul nauwara da kallo
saboda tabbas yanzu ta tabbatar da abinda take
zargi wato babu makawa kawarta ta kamu da son
saurayin da fiyeda shekaru shida da suka gabata
ita ta kamu da tsananin sonsa
nantake tafada cikin kogin tunani…………..
soyayyar sarauniya anisa ga jarumi hatyan ta
samo asaline tun kimanin shekaru shida da suka
shude wata rana sa'adda tayi badda kama ta
shiga birnin bindal amatsayin yar kasuwa suna
shiga cikin birnin sai keken dokinsu ya sami
matsala yazamana cewa wilin tayar keken ya
karye nan take aka basu shawara sukai gidan
sarkin makera a gyara musu
batare da bata wani lokaciba akayi musu jagora
izuwa gidansu jarumi hatyan awannan lokaci
anisa ta lullube gaba daya jikinta da wadansu
bakaken tufafi masu kauri kuma ta rufe fuskarta
da wani bakin kyalle mai dan shara shara
idanunta kadai ake iya gani
da isarsu sarauniya anisa kofar gidansu jarumi
hatyan sai sukaga mahaifinsa a zaune acikin
makera yanata aiki itadai sarauniya anisa sai
tayi zamanta acikin keken doki hadimanta guda
hudu da suke tareda ita sai suka sauko sukaje
wajen baban hatyan suka sanar dashi matsalarsu
nan take sarkin makera yaje ya duba wilin tayar
daya karye sannan ya dubi shugaban hadiman
yace
nawa zaku biya na sauya muku wannan taya da
wadda ta fita kwari wacce zata iya shekara
goma nan gaba ba tarda ta sami matsalaba?
kodajin wannan tambayar sai hadimin ya juya ya
dubi sarauniya anisa don yaji ra'ayinta
kawai sai tayi murmushi tayiwa hadimin magana
cikin yaren kurame
hadimin ya juyo ya dubi sarkin makera yace
uwargidana tace tanaso ka sauya mata gaba
daya tayoyi hudun kuma ka fadì nawa kake
bukata zata biyaka
kodajin wannan batu dai mamaki ya turnuke
sarkin makera yace aransa duk yadda akayi
wannan mata ba 'yar kasuwa bace wadda ta
saba juya taro da sisi
domin shi dan kasuwa baya kashe kudi haka
sai dai basarake
sarki makera ya dubi hadimin yace
ku biyani dinare dari uku
hadimin ya dubi sarauniya anisa ita kuma saita yi
masa inkiyar ta yarda kawai
sai hadimin ya bude jaka ya fiddo dinare mai
yawa ya kirga dinare dari ukun ya baiwa sarkin
makera
sarki makera ya dubi yaransa biyu dake faman
aiki acikin makera wadanda suka kasance samari
masu karfi yace
kuzo ku kwance tayoyin keken dokin nan domin a
daura sababbi
ba tareda bata wani lokaciba sai kartin biyu suka
debo kayan aiki suka fara kokarin kwance
notikan da suka daure tayoyin amma sai notikan
sukaki kwantuwa saboda dukkansu sunyi tstasa
tuni awannan lokaci anisa ta sauko daga kan
keken dokin ta koma gefe daya ta zauna tana
kallon abinda yake faruwa
nan fa wadannan katti suka gaji ainun batareda
sun iya kwance koda noti dayaba
al'amarin daya ya bai wa kowa mamaki kenan awajen
shikuwa sarkin makera sai yazo ya dudduba
keken dokin ya kare masa kallo tsaf sannan ya
dubi anisa yace
ranki ya dade amma wannan keken dokin a birnin
sin aka siyoshi ko?
cikin mamaki babban hadimin ya dubi sarkin
makera yace
yaya akai ka sani?
sarkin makera yayi murmushi yace
ai babu wata babbar kasa aduniya wacce banje
cikinta na koyi aikin kiraba
wadannan yara nawa basu da karfin da zasu iya
kwance notin birnin sin amma akwai wani yarona
guda daya zai iya yanzu baya nan amma yana
daf da dawowa
kodajin wannan batu sai mamaki ya kama anisa
ta kirawo babban hadimanta tayi masa rada
akunne sannan ya dawo wajen sarkin makera
yace uwargidana tace
idan her yaron naka yazo ya iya kwance tayoyin
wannan keken dokin zata baka ninki uku na kudin
gyaran da zata biya yanzu
idan kuma ya kasa kwancewa to ita zata kwance
da kanta,
amma ba zata baka ko sisi ba a kudin gyara da
kayi
ba tareda shakkar komai ba sarkin makera yayi
murmushi yace
nayarda da wannan sharadi
gama fadin hakan keda wuya saiga jarumi hatyan
ya dawo daga farauta yana sanye da wata
tsohuwar riga wacce ta matseshi sosai
awannan rana ya fafata yaki da wani murgujejen
zaki adaji dakyar ya kasheshi
kuma zakin yayi masa wani rauni guda daya
agadon bayansa
tundaga nesa hatyan ya karewa kowa kallo tsaf
akofar gidan nasu
koda yaga wadannan yaran mahaifinsa guda biyu
atsaye agaban keken dokin suna ruke da kayan
aiki sun hada zufa saiya gane abinda ke faruwa
tun kafin ya iso gurin ya karewa anisa kallo
domin ya gano budurwace ko babbar mace
amma saiya kasa tunda arufe jikinta yake da
tufafi masu kauri kuma ta rufe fuskarta
da isowarsa ko kala baice da kowa ba saiya karbi
abin kwance notin daga hannun daya daga cikin
kattin biyu ya fara kokarin kwancewa
dafarko saiyaji notin yaki kwantuwa amma daya
tara karfinsa waje guda sai nan da nan notin ya
juya alokacinda kwanjin hannayensa ya kumburo
rigar tasa ta dare
nanfa anisa ta kura masa idanu tana mamaki
azatonta bazata sami sadaukin da zai iya
kwance wadannan notikan ba........sai gashi ni AA Misau na
kunce kuma anan zan tsaya sai wani jikon idan baku sake
gajiyaba



TARKON MUTUWA
Abdulaziz Sani madakin Gini
Post:- AA Misau
Littafi na Shida 6
Part 6 D
.
.
lokacinda anisa tazo nan atunaninta sai ta juya ta
koma cikin gidan sarautarta, ta wata boyayyiyar
hanya ta musamman
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU ABIRNIN
SARAUNIYA ANISA BAYAN TA SAMI NASARAR
FITAR DA SU HATYAN IZUWA NAHIYAR GABANSU
Al'amarin jarumi hatyan kuwa tunda suka fada
cikin nahiyar gaba sai suka tsinci kansu cikin
farinciki gami da kwanciyar hankali tamkar basu
da wasu makiya dake farautarsu
tunda suka nausa acikin dajin suna tafiya her
tsawon yini guda basu hadu da wani mugun
abuba sau tari idan ma suka hango wata dabbar
daji mai hadari kafin su risketa sai ta sauya hanya
ta basu wuri
abu daya ne ya sosa musu rai ba komai bane
face sauyin yanayi basu taba ganin daji irin
wannan ba hatta duwatsu da bishiyoyi da
tsuntsayen ma ba irin wanda suka saba gani bane
sai da rana ta fadi sannan su hatyan suka yada
zango abakin wata korama mai dauke da ruwa
garai garai gwanin ban sha'awa yake saboda ni
imarsa ta kyawawan bishiyoyi tsirai gamida
koramu
bayan hatyan da sadirat sunci abinci sun sha
ruwa sai suka zauna abakin wannan korama suna
kallon yadda ruwa ke kwaranya acikin nishadi
tsawon yan dakiku dayan su baice uffan ba
daga can sai sadirat ta dubi hatyan alokacinda
idanunta suka ciko da kwalla tace
yakai dan uwana yanzu shike nan bamu da ikon
komawa birnin mu bare har mu nemi inda kabarin
iyayenmu yake mukai musu ziyara?
kodajin wannan tambayar sai nan take shima
hatyan yaji idanunsa sun ciko da kwalla kafin ya
ankara hawaye ya subuto masa don haka sai ya
janyo sadirat ya rungumeta yace
ki kwantar da hankalinki yake yar uwata nayi miki
alkawarin komai daren dadewa sai mun koma
birnin bindal mun dauko fansar ran mahaifinmu,
kuma ina mai tabbatar miki da cewa bokana na
nan araye bai mutuba
kuma nasan ya binne gawar iyayenmu a inda
babu wanda ya. sani
kodajin wannan batu sai farinciki ya lullube
sadirat ta janye jikinta daga nasa ta dubeshi cikin
murmushi da nufin tace wani abu
kwatsam sai suka ji wani irin gurnani mai ban
tsoro ya cika dajin daga kowacce kusurwa kuma
gurnanin ya dinga karuwa yana kusanto su
al'amarin daya firgita sadirat kenan ta koma
bayan hatyan ta kankameshi
lokaci guda sai suka hango wadansu manyan
zakuna sama da guda dubu daga gabasa da
yamma kudu da arewan dajin
cikin zafin nama hatyan ya mike tsaye zumbur
yana mai goya sadirat a gadon bayansa ya ruga
izuwa cikin koramar dake gabansu,
suna fadawa cikin koramar sai suka ga ashe
acike takeda wadansu irin manya manyan kadoji
tunda suka zo duniya basu taba ganin kadoji
masu girmansu ba
kafin hatyan ya yi wani yunkuri tuni wani kada ya
make sadirat da jelarsa
sadirat tayi sama ta fada can gefen koramar ta
baje akasa sumammiya jini na zuba akanta
cikin zafin nama hatyan ya daka tsalle ya kamo
reshen wata bishiya dake cikin koramar yana
reto akanta
ai kuwa sai wani kada ya wangame bakinsa ya
kawo masa hadiya
hatyan ya daka tsalle daga kan bishiyar ya
kaucewa harin kadar
koda kadan ya cafi bishiyar sai ya gatsata ta
rabe biyu duk da cewa kaurinta yafi kamu ashirin
hatyan na fadowa kasa sai ya tsinci kansa
atsakiyar miyagun zakuna sama da guda dubu
uku
koda ya dubi can gefensa ya hango 'yar uwarsa
sadirat kwance cikin mugun hali sai ya kwarara
uban ihu cikin tsananin fushi yayi wuf ya zare
takobinsa ya afkawa zakunan
SHIN JARUMI HATYAN ZAI KUBUTA DAGA
HANNUN WADANNAN MIYAGUN ZAKUNA DA
KADOJI?
WANE HALI 'YAR UWARSA SADIRAT KE CIKI! ?
ZATA RAYU NE KO MUTUWA ZATAYI?
YAUSHENE HATYAN ZAI SAKE SADUWA DA
ANISA DA KUMA BADI'ATUL NAUWARA?
YAYA ZAIYI DA SOYAYYAR MATAN BIYU?
YAUSHENE ZAI DAWO BIRNIN BINDAL DON
DAUKAR FANSA AKAN SARKI SHAMSAL?
MU HADU ALITTAFI NA BAKWAI DON JIN
CIGABAN WANNAN LABARI,

Post a Comment

Previous Post Next Post

Contact Form