π©π©π§π¦*JARIRAI*π¨π¨π§π§
.
✏Posted by Md Abubakar Islam
.
Page 01
.
Zamu fara wannan littafin yau Insha Allah sannan a kullum zai zo muku sau Ιaya da misalin Ζarfe 12:00pm na rana.
Insha Allah bayan mun kammala wannan littafin zamu fara posting Ιin littafin Heedayah
.
Ku kasan ce damu a kullum a koda yaushe, Mungode ππ
.
Lamarin ya fara ne a wata ranar Laraba da safe ina ta sauri dan fita aiki, kasancewar yau ranar ina da wasu manyan ayyuka da zan gabatar.
Ina Toilet ina murza wanka da injin Bature mai tunkuΙo ruwa, (Shawa), kamar almara kunnuwana suka fara jiyo min sautin kukan *JARIRAI* daga wajen Ιakin, nan da nan na dakata da murza soson wankan da na ke yi a jikina nayi tsai! Ina sauraro dan tabbatar da saΖon da kunnuwan nawa suke aikewa da ΖwaΖwalwata.
Da gaske dai kukan *JARIRAI* ne na ke ji, Ras! Ζirjina ya buga da Ζarfi, ba komai ne kuma ya saka ni cikin wannan yanayin ba face sanin da nayi cewar Matata ko Ιatan wata bata taΙa yi ba tsawon shekaru bakwai da yin aurenmu balle in saka ran ita ce cikinta ya tsufa ta haife shi yanzu-yanzu.
Kukan Jariran ya cigaba da ratsa dodon kunnena ya na Ζara hauhawar min da farashin faΙuwar gaba.
Nan da nan nayi jifa da soson wankam na shiga Ιauraye jikina babu shiri, dukda cewar ban gama wankan ba hakannan na janyo Ζaton Tawul na rufe jikina da shi nayi waje da sauri dan in ga zahirin abin da kunnuwana ke jiye min.
Matata Nuratu na ci karo da ita ta yi Ιai-Ιai a kan faffaΙan gadonmu hannunta riΖe da waya, ko ba a faΙa min ba na san abin da take aikatawa da wayar, chating ne wanda bata da aikin da ya wuce shi a kullum.
Da sauri na isa gabanta na tsaya ina maida numfashi tamkar wanda ya ci tseren gudun famfalaΖi.
"Nuratu a ina aka samu *JINJIRI* a gidan nan?"
Na watsa mata tambayar ina zare idanu tamkar maye ya ci yaji.
Wani irin kallo take watso min itama wanda ya fi kama da na wacce aka zo wa da maganar rainin hankali.
Bakinta a mele ta ce, "Jinjiri kuma? Ban gane wannan tambayar taka ba malam, ko ko dai abin naka ne ya motso maka ka zo ka sauke min kwandon rashin mutunci akan rashi haihuwa kamar yadda ka saba?"
Da sauri na girgiza kai, "Kinga Nuratu dan Allah ba wannan maganar ba ce ta kawo ni, babu ma muhallinta a yanzu. Wai ba ki ma lura da yanayin da na fito daga wankan ba ne? Wallahi kukan *JARIRAI* ne ya ishe ni shine na fito inga ko baΖuwa muka yi."
Kallo na ta yi sama har Ζasa, "Hmmm! Maza kenan kun san takan bariki! In kuka so latsa matayenku kun fi kowa iya shan babbar kwana... To ai sai ka koma ka Ζarasa wankanka, *JARIRI* kuma wata kila in ka fito ka tarar na haife maka shi tunda har kukansa ke yi maka gizo a kunne."
Na fuskanci dai Nuratu ba ta Ιauki maganar tawa da muhimmanci ba, dalili kenan da yasa na Ζara takawa na nufi falo dan dai in Ζara tabbatarwa ko ba baΖuwar mu ka yi ba, dan ni fisabilillahi na ji kukan jariri, kuka ba irin wanda na saba ji daga bakunan *JARIRAI* ba, wannan kukan na musamman ne, cike yake da ban tsoro da haifar da fargaba.
Na isa falon na shiga dube-dube tamkar Ιarawon da ya shigo yin sata, babu kowa kuma babu komai, falon yana nan yadda yake bai karu da komai ba bai kuma ragu da koda silin tsinke ba.
Har na yunkura da nufin sake komawa dakin namu dan in koma Toilet in Ζarasa wanke kumfar wankan da ta riga ta bushe a jikina sai na sake jin wata muryar Jaririn ta canyare da kuka...
Tamkar yadda idan Zakara Ιaya ya yi cara sauran Zakaru suke amshewa su yi ta yi, haka na ji muryoyin *JARIRAI* sun amshe da kukan su ma.
Ai sao na ji ina neman yanke jiki in faΙi, na daure dai na Ζwaci Ζarfin gwiwa na koma Ιakin da sassarfa, ashe abin da zan gani shine zai kusan yin ajalina ta hanyar tsoratani.
Babu Nuratu a kwance a gadon kamar yadda na fita na barta, maimakon hakan ma sai wani kyakkyawan *JARIRI* shimfide a kan gadon namu cikin shigar alfarmar sai faman tsandara ihu yake ga wani farin abu mai kama da ruwan nono na ΙuΙΙugowa daga babban Ιan yatsansa da ya ke cikin bakinsa.
Nayi yunΖurin juyawa cikin zafin nama dan na fita a guje amma sai na ji tamkar an riΖe min Ζafafuna da dabaibayi. Jikina ya shiga rawa kwatankwacin tsohon Baushen da ya ji kidan farauta, bakina da zuciyata suka kulle balle in samu damar halarto addu'ar neman tsari daga shaidanu.
Abin da ya Ζara gotar min da saitin ΖwaΖwalwata shine ganin yadda jinjirin ya taso cikin iska shuuu tamkar wanda aka sa hannu aka dauko shi, a daidai saitin kaina ya tsaya yadda zan iya ganin sa sosai.
A yanzu babu riga a jikinsa, cikinsa kuma a Ιule jini na ta ΙulΙula yaron yana cigaba da kukan da yake Ζara zare min Ζarfin gwiwata.
Baki sosai jinjirin ya buΙe ya soma magana cikin kukan da ya ke yi.
"Sunana *BABUL* ni ne Ιanka na farko! Dan me yasa za ka ji tsoro na? Shin ba ka so wannan ziyarar ta mu gare ka ba ne ko me? Ta ya ya *UBA* zai ji tsoron 'ya'yansa?
Ka sani ya kai Babanmu, yanzu adadin mu mun kai mu Ιari Bakwai da Sittin da Biyu, kuma sannu a hankali kowa zai kawo maka ziyara Ιaya bayan Ιaya har zuwa kan Autarmu, kuma kowa da irin sigar da zai bayyana da ita gareka, musamman autarmu tafi kowa fitina, sai ka yi haΖuri da irin sigar da za ta zo maka...
Wannan zuwa na ne a matsayi na na jagoran tafiya, na zo maka da saΖon cewa ka shirya kyakkyawar tarba ga sauran 'yan uwana da su ke tafe gareka, kafin daga bisani mu zo maka gaba Ιayan mu bayan kowa ya kawo maka tasa ziyarar shi kadai..."
Yana gama faΙin haka na neme shi sama ko Ζasa na rasa, sannan kuma kamar an yi ruwa an Ιauke haka na ji Ιif komai ya tsaya, kukan *JARIRAN* da na ke jiyowa sama-sama shima ya Ιauke Ιif.
Sannu a hankali kuma ganina ya koma dishi-dishi, sautin da kunnuwana ka iya ji shi ma ya dusashe, sai na ji komai na jikina ya saki tamkar an kwance Akuyar da ta shekara a Ιaure.
Na zame na zube Ζasa sharab bakina na ambaton sunan matata Nuratu! Nuratu!!!
•
•
•